@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
ALLAH KA RABA MU DA CIWON JAHILCI
Turba wata dunqulalliyar qasa ce wacce 'yan Shi'ah ke amfani da ita wajen sujadah. Ita wannan qasa ana iya daukarta wajen tafiya don yin amfani da ita wajen sallah yayin da mutum ya sami kansa cikin sallah a gurin da bai kamata ayi sujadah ba.
Kowa yasan cewa fuska qasa ita tafi komai soyuwa wajen Allah yayin sujadah, saboda haka yin sujadah a kanta yafi komai falala.
Annabi (S. A. W. W) ne ya fara yin sujadah a kanta, ko da shike a wancan lokaci sukan kirata ne ta KUMRA. Yin koyi da aikinsa kuwa shine asalin sunnah.
Ku biyo mu cikin wannan hadisi
25978- حَدَّثَنَا عَفَّانُ ، حَدَّثَنَا وُهَيْبٌ ، قَالَ : حَدَّثَنَا خَالِدٌ ، عَنْ أَبِي قِلَابَةَ ، عَنْ بَعْضِ وَلَدِ أُمِّ سَلَمَةَ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ : " يُصَلِّي عَلَى الْخُمْرَةِ " .
Affan ya bamu labari, Wuhaib ya bamu labari yace, Khalid ya bamu labari daga baban Qilaabata, daga sashen 'ya'yan Ummus-Salamata, daga Ummus-Salamata cewa Annabi (S. A. W. W)
" YA KASANCE YANA YIN SALLAH AKAN KUMRA ."
(MUSNAD-NISAA'I)
Amma a wannan lokaci sai ya zamana cewa wasu mutane sun Jahilci 'yan Shi'ah kan dabbaqa wannan sunnah, har ma suna gani kamar wata sabuwar bid'ah aka qirqiro.
ALLAH KA RABA MU DA CIWON JAHILCI
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
4th October, 2020/ 17th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Assalamu alaikum amma wannan hadisin a wanne littafin yake
ReplyDeleteAssalamu Alaikum Allah ya saka da Alkhairi
ReplyDeleteAmma munason sanin Hadith din a wanne littafi zamu sameshi (reff.)