Amma yan arewa ku fito mu fadawa kanmu gaskiya, ka tsaya kayi tsam kayi tinani, yau ace kungiyar SHI'A wata kungiyar addinin kirista ce a kudu masu bin wata mazhaba a addinin kirista, aka je aka yi musu wannan Kisan kamar kiyashi? Kana tinanin yankin kudu zasu yadda, kana tinanin kungiyoyin addinai na duniya zasu yadda, kana tinanin American da kake cewa tace ayi kaza abar kaza zata bar wannan Kisan ya tafi a banza?
Yankin kudu zasu fito gaba daya ne, zasu ajiye rabe-raben kawunan dake tsakanin su su fito su cika kasar nan da muguwar zanga-zangar da hankalin duniya sai ya dawo kan Nigeria.
Kar kayi tinanin sojoji sun kashe yan SHI'A ne saboda aƙidar da suke ta sabawa ta musulunci, aa su a zuciyarsu ji suke sun kashe musulmai Kuma yan arewa, Kuma sun tabbatar babu abin da zai faru. Amma basu duba human rights din da suke tutiya dashi ba, suka dinga zubar dasu Kamar kiyashi, Kuma aka daure jagoran su aka hanasu belin sa.
Yaushe kaji human rights tayi Magana? Yaushe kungiyoyin turawa kaji sunyi magana akan rashin daidai.
Kaine kake murna an kashe wadanda baka san aƙidar su, Amma su murna suke sun rage yawan yan arewa. Tinda su basa banbance wata izala, tijjaniyya, salafiyya, SHI'A, kai daka fahimci addini kaine zaka rabe wadannan.
Yan kudu babu wata wayewa da suka fimu, Amma sun fimu kokarin san junan su da kokarin hadin kai, duk tsanar da sukayiwa nasu idan ka shigo daga waje ka taba nasu gaba daya zasu hayayyaƙo maka.
Amma mu arewa har kokarin ganin laifin junan mu muke, farin ciki kake kaga naka ya Shiga masifa kayi murna.
Ka daina yabon su, basa Sanka Muma basa sanmu, neman gazawar mu suke suci mana mutunci, kayi kokarin kaunar naka kawai. Ko kuso ko karka so sun fimu kokarin jajircewa wajen ƙwatowa kansu yanci.
YUNUSA YELLOW ya isheka misali, Akan laifin da bashi kadai yayi ba, sun dauke shi sun daure shi a wajen su suna zargin sa da laifin sace musu yarinya. Kaf arewa akwai wanda ya isa ya daure musu yaron s