Yadda Zaben Qananan Hukumomi Ya Gudana A Jihar Bauchi: "Mudu Zamu Aro Daga Makota, Don Auna Zabubbukan Mu" Cewar Hon. Abdulrazak Nuhu Zaki


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen gunadanar da zabubbukan qananan hukumomi a jihar Bauchi kamar yadda mai girma Gwamnan jihar ya alqawaranta an sami wani furuci wanda ya fito daga bakin gogaggen dan siyasar PDP ta jihar Bauchi Honourable Abdurrazaq Nuhu Zaki. 


Cikin furucin nasa yake cewa, 


" ZA MU ARO MUDU DAGA MAQWABTAN JIHOHINMU NA KANO DA JIGAWA DON AUNA ZABUBBUKANMU ."


Wannan furuci nasa ya girgiza 'ya'yan jam'iyyar APC yadda suke hasashen cewa ba za ayi musu adalci ba ganin jam'iyyar dake mulki a Kano da Jigawa na APC ne kuma duk sune aka ce sun lashe kujerun qananan hukumomi dana gundumomi. 


Duk da haka jam'iyyar adawa ta APC a jihar Bauchi tayi alwashin fitowa qwansu da qwarqwatarsu wajen wannan zabe bisa qarfi qwiwa na ganin mafiya rinjaye a majalisar jihar 'ya'yan APC ne, yayin da jam'iyyar PDP ke ganin ita ke da Gwamna. 


     DA GASKE ANYI ZABE 


Ba kamar yadda 'ya'yan jam'iyyar APC ke fada bane cewa wai ba ayi zabe cikin jihar ba, domin naji Alh Uba Ahmad Nana shugaban jam'iyyar APC na jihar Bauchi na cewa ba ayi zabe ba. Har ma yana misalta abinda akayi a matsayin diramar su 'Dan Ibro, kuma yake cewa ko su 'Dan Ibro ma basu taba yin irin wannan diramar ba. 


Cikin jawabin nasa ya bawa 'ya'yan jam'iyyar tasu haquri na abinda akayi musu, kuma ya dau alwashin shigar da qara gaban kotu don ta nema musu haqqinsu. 


Abinda ya tabbata dai shine anyi zabe a jihar Bauchi ranar asabar 17-10-2020, ko da kuwa ba abinda aka zaba aka bayyanar da shi ba. 


Dalili wannan magana kuwa shine, Senata Bala Abdulqadir qauran Bauchi (Governor) yayi tattaki shi da matarsa har zuwa mazabarsa a qaramar hukumar Alqaleri sunyi zabe har ma an watsa ta kafafen sada zumunta na zamani, kuma a matsabar dake gundumarmu ma anyi zabe har an qirga ansa hannu kafin subar gurin. 

Zuwa wannan lokaci dai an gama rantsar da shugabannin qananan hukumomi 20 dake jihar Bauchi da kuma kansilolinsu, kuma dukkansu 'ya'yan jam'iyyar PDP ce. Sannan mai girma Gwamna yayi alwashin sake musu mara don su sami damar yin ayyuka a mazabinsu da ma jiha baki daya. 


      QORAFE-QORAFE 


Dama siyasa ta gaji haka. Bayan bayyanar da sakamakon zabe an sami mutane daban-dabam sun fito don tofa albarkacin bakunansu. 


Wani daga bangaren PDP godiyarsa ya nuna ga dukkan al'ummar jihar Bauchi da ta gane ta fito ta zabi jam'iyyarsu bisa yaqinin ita ce za ta iya cire musu kitsensu daga wuta. 


Na bangaren APC kuma suna Allah ya isa ne kan wannan nuna fin qarfi, fashi da kuma fyade da akayi musu suna bayyana su a matsayin marar sa adalci. Na bangaren PDP kuma sai sam-barka suke nunawa.


Yayin da aka bayyanar da nasarar 'ya'yan jam'iyyar APC a jihar Kano da Jigawa na PDP sun nuna cewa ba ayi musu adalci ba, na APC kuma na murna cewa sunyi nasara. 


Ko da aka bayyanar dana jihar Bauchi ma 'ya'yan jam'iyyar PDP tayi farin ciki, yayin dana APC ke fassara su a matsayin marar sa adalci. 


         TAWA FAHINTAR 


Ganin yadda kowanne bangare ke nuna rashin adalcin bangare kamar yadda suke zargi junansu yasa nake cewa in har rashin adalcin da suke fada ya tabbata ga dukkan bangare, to, dukkansu sun zama marar sa adalci kenan. 


Idan kuwa hakane sai nace lalle ko a tsarin konsitushan basu cancanci zama shugabannin al'umma ba ballantana a muslimci, domin sun rasa (qualities) na shugabanci (leadership). 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

         08126385470


20th October, 2020/ 3rt Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post