Masu zanga-zangar #EndSars wanda suka shafe makonni suna yi a manya-manyan biranen kasar nan sun kone Police Station a garin Lagos, sun balle gidan Yari masu laifin gidan yarin sun gudu a Jahar Ekiti, sun kuma kona Motocin Dangote guda biyu da lalata kayan Gwamnati da dama duk a lokacin gudanar da zanga-zangar kira da a soke Rundunar Sars, duk da cewa Gwamnatin Tarayyar ta sanar da cewa an rushe Rundunar, amma har yanzu da sunan "Masu Zanga-zanga" ake kiran su.
Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) wanda ake tsare da Jagoransu fiye da shekaru biyar suna fitowa zanga-zangar a garin Abuja dama sauran wasu garuruwan kasarmu Nijeriya domin kira ga gwamnatin ta saki musu malaminsu da kotu ta saka tun shekaru uku dasu gabata ana bude musu wuta da harsasai masu rai, Barkonon tsohuwa da ruwan zafi ana cin zarafinsu duk da cewa su basu taba kona wani waje ko lalata wani abu na Gwamnatin ko mallakin wani ba, kullum suna zanga-zangarsu ne cikin lumana amma an kirasu da sunan "Yan Ta'adda".
Tun a nan Mutane ya kamata su gane cewa ba wai dama tare hanya bane yasa aka kashe yan Shi'a da kuma kama Jagoransu a shekarar 2015, dama chan sun shirya hakan ne domin ganin sun murkushe duk wani abu da ya shafi Harka Islamiyya domin su shafe mu kwata-kwata. Masu Zanga-zangar #EndSars har yanzu Gwamnatin Nijeriya cigaba da basu hakuri take yi da rarrashinsu duk da cewa irin barnar da suke yi na lalata kayan Kasa shi ake ta kokarin jona ma yan Shi'a irin barnar a lokutan baya domin a samu hujjar kashesu, Jami'an tsaro da kansu suke barnata wani kaya na Gwamnatin domin su nuna cewa yan Shi'a ne suyi hakan, amma yau ga wasu kowa ya tabbatar da suna aikata barnar kuma ana cigaba da basu hakuri. Allah ya sakawa Sheikh Zakzaky da irin Wannan zaluncin da kuke yi masa.