@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA YAWA DAGA CIKIN SAHABBAI BASU JI DADIN HAKAN BA
Al'amarin Imamancin Imam Ali (A. S) ba ya auku bisa hatsari bane, kuma ba bisa son zuciyar Manzon Allah (S. A. W. W) bane. Wasiccin ya kasance ne daga Allah (T) wanda Annabi (S. A. W. W) ya kasance mai bayyanar da shi gare mu.
Ibn Abbas (R. A) ya bayyanar da haka cikin wani hadisi wanda za mu kawo shi kamar haka,
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
لي، الأمالي للصدوق ابْنُ سَعِيدٍ عَنْ فُرَاتٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ أَحْمَدَ الْهَمْدَانِيِّ عَنِ الْحُسَيْنِ بْنِ عَلِيٍّ عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ سَعِيدٍ الْهَاشِمِيِّ عَنْ عَبْدِ الْوَاحِدِ بْنِ غِيَاثٍ عَنْ عَاصِمِ بْنِ سُلَيْمَانَ عَنْ جُوَيْبِرٍ عَنِ الضَّحَّاكِ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ قَالَ:
Ya zo cikin Amali lis-Sudduq Ibn Sa'eed , daga Furata daga Muhammad Bn Ahmad Al-Mahadaniyyu , daga Hussaini Bn Aliyu, daga Abdullahi Bn Sa'eed Al-Hashimiy, daga Abdulwaaheed Bn Ghiyaas , daga Aaseem Bn Sulaiman, daga Juwaibeer, daga Dhahhaak, daga Ibn Abbas (R.A) yace,
صَلَّيْنَا الْعِشَاءَ الْآخِرَةَ ذَاتَ لَيْلَةٍ مَعَ رَسُولِ اللَّهِ ص فَلَمَّا سَلَّمَ أَقْبَلَ عَلَيْنَا بِوَجْهِهِ ثُمَّ قَالَ
" A wani dare munyi sallar Isha'i tare da Manzon Allah (S. A. W. W) , yayin da muga gama sai ya juyo da fuskarsa (S. A. W. W) gare mu, sannan yace,
أَمَا إِنَّهُ سَيَنْقَضُ[1] كَوْكَبٌ مِنَ السَّمَاءِ مَعَ طُلُوعِ الْفَجْرِ فَيَسْقُطُ فِي دَارِ أَحَدِكُمْ فَمَنْ سَقَطَ ذَلِكَ الْكَوْكَبُ فِي دَارِهِ فَهُوَ وَصِيِّي وَ خَلِيفَتِي وَ الْإِمَامُ بَعْدِي
" AMMA CEWA FA SHI DA SANNU WANI TAURARO 🌟 ZAI YANKO DAGA SAMA YAYIN KETOWAR ALFIJRI YA FADO CIKIN GIDAN 'DAYAN KU. TO, DUK WANDA WANNAN TAURARO 🌟 YA FADO CIKIN GIDANSA, TO, SHINE WASIYYINA KUMA KHALIFANA KUMA IMAMI A BAYANA ."
فَلَمَّا كَانَ قُرْبُ الْفَجْرِ جَلَسَ كُلُّ وَاحِدٍ مِنَّا فِي دَارِهِ يَنْتَظِرُ سُقُوطَ الْكَوْكَبِ فِي دَارِهِ وَ كَانَ أَطْمَعَ الْقَوْمِ فِي ذَلِكَ أَبِي الْعَبَّاسُ بْنُ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ فَلَمَّا طَلَعَ الْفَجْرُ انْقَضَّ الْكَوْكَبُ مِنَ الْهَوَاءِ فَسَقَطَ فِي دَارِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص لِعَلِيٍّ
" Yayin da alfijri ya kusanto sai kowanne dayanmu ya zauna a cikin gidansa yana sauraron fadowar wannan tauraro 🌟 a gidan nasa . Ya kasance mafi kwadayin mutane game da haka (son wannan khalifanci) shine baban Abbas Bn Abdul-Mudallib. Yayin da alfijri ya keto sai wannan tauraro 🌟 ya yanko daga sama ya fado cikin gidan Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S). Sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya cewa Aliyu,
يَا عَلِيُّ وَ الَّذِي بَعَثَنِي بِالنُّبُوَّةِ لَقَدْ وَجَبَتْ لَكَ الْوَصِيَّةُ وَ الْخِلَافَةُ وَ الْإِمَامَةُ بَعْدِي
" YAA ALIYU ! NA RANTSE DA WANDA YA AIKO NI DA ANNABTA , HAQIQA WASICCI DA KHALIFANCI DA IMAMANCI YA WAJABA GARE KA A BAYANA ."
فَقَالَ الْمُنَافِقُونَ عَبْدُ اللَّهِ بْنُ أُبَيٍّ وَ أَصْحَابُهُ لَقَدْ ضَلَّ مُحَمَّدٌ فِي مَحَبَّةِ ابْنِ عَمِّهِ وَ غَوَى وَ مَا يَنْطِقُ فِي شَأْنِهِ إِلَّا بِالْهَوَى فَأَنْزَلَ اللَّهُ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى
Sai munafukai (su) Abdullahi Bn Ubaiyu da sahabbansa suka ce,
.
" Haqiqa Muhammadu ya bace cikin soyayyarsa ga dan amminsa kuma ya halaka. Ba ya magana cikin sha'aninsa sai bisa son zuciyarsa. "
Sai Allah ya saukar da,
وَ النَّجْمِ إِذا هَوى
" INA RANTSUWA DA TAURARO YAYIN DA YA FAKU. "
يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ وَ خَالِقِ النَّجْمِ إِذَا هَوَى-
Allah mai girma da daukaka na fada ne game da dabi'ar wannan tauraro 🌟 yayin da ya faku .
ما ضَلَّ صاحِبُكُمْ وَ ما غَوى
" ABOKINKU (Muhammad S. A. W.W) BAI BACE BA KUMA BAI HALAKA BA . "
يَعْنِي فِي مَحَبَّةِ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ ع-
Yana nufi (bai bace ba) cikin soyayyar Aliyu Bn Abiy 'Dalib (A. S).
وَ ما يَنْطِقُ عَنِ الْهَوى
" KUMA BA YA MAGANA BISA SON ZUCIYARSA ."
يَعْنِي فِي شَأْنِهِ-
Ma'ana cikin sha'aninsa (A. S).
إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحى.
" BAI KASANCE (abinda ya fada) BA FACE WAHAYI DA AKAYI WAHAYINSA (gare shi) ."
(1) النجم: (53- 1).
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج35، ص: 273
Wannan nassi ne wanda ke tabbatar da cewa Imam Ali (A. S) shine wasiyyi kuma khalifan Annabi (S. A. W. W) a bayansa.
Duk Sahabbai sun san haka kuma sun fahinci bayanin da Annabi (S. A. W. W) yayi, shi yasa ma munafukai daga cikinsu ke zargin Annabi (S. A. W. W) da bin son zuciya tare da jingina masa bata .
Shine Allah (T) ya wanke shi (S. A. W. W) tare da tabbatar musu cewa wannan wasicci daga gare Shi (S. W. A) ne.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
08126385470
26th October, 2020/ 10th Rabi'ul-Awwal, 1442.