Wacce Nake Son Aura! Labari Mai Ratsa Zukata Tsakanin Sister Da Brother!!

 



Kyakkyawa ce kyau mara misaltuwa, wajen hali, sakamakon irin tarbiyar da ta samu a gidansu daga mahaifanta guda biyu. Ko ba komai, mahaifinta wani mutum ne ma’abocin addini, mai riko da koyarwar tsarkakan bayi, daidai gwargwado ya karantu, dan haka ya kasance mai aiki da abin da ya karanta. Kai in takaice muku, shi mahaifin nata irin mutanen nan ne da matansu suke musu kirari ta hanyar ce musu ‘Mazajen goyo da majanyi!’

Ka san kuwa idan har mata, wadanda aka sansu da yi wa maza kirari da cewa “Namiji ba dan goyo bane” sai ka ji wata tana cire nata mijin ta hanyar cewa shi ‘Namijin goyo da majanyi’ ne ma, kun san lallai namijin nan irin mazan nan ne da suka debi soyayyar tsakani ga Allah tun ana yarinta, har gashi ‘yarsu ta tasa ta isa aure, har ma ta sameni a matsayin saurayi, amma wancan soyayyar tasu (iyayen) na nan a matsayin budurwa, duk kuwa da tsufan da suka yi bayan tasawar kyakkyawar yarinyarsu.

A zahiri, na iya shaida cewa mahaifin wannan wacce nake so din, irin mazan nan ne da Annabi (S) yace: “Mafiya alkairin mutane daga cikin al’ummata sune wadanda ba su tsawwalawa iyalansu, kuma ba su zaluntarsu.” Saboda a iya bincikena ban taba jin ko a labarum tsegumi irin na matan gidan biki, ko kuma na mazan dandali, cewa sun taba samun sabani da matar tasa wacce yake matsanancin sonta kamar yadda take sonsa ba.

Ita ma mahaifiyar matar da nake son aura, irin wannan matan ne da Manzon Allah (S) yake cewa: “yana daga cikin dacen mutum ya samu mace managarciya.” Haka ma Amirulmuminin Ali ‘Dan Abudalib (AS) yana cewa; “Mace tagari ta fi alkairi akan mutum dubu da ba nagargaru ba.” To da gasken-gaske bincikena ya nuna min cewa ita wannan mahaifiyar tana cikin wadannan mata na gargarun da Allah ya ma sirikina baiwa da ita. 

Kai, sarkuwar tawa fa a iyakan sanina, bata yarda ta kasance daga matan nan da za su rasa maceci a ranar Lahira ba, kamar yadda aka ruwaito daga Imam Muhammad al-Bakir (AS) yana cewa: “Babu wani maceci ga mace wanda zai tseratar da ita daga Ubangijinta face yardar mijinta (a gareta).” To sarkuwar tawa ta kasance tana iyakar yinta wajen ganin ta samu yardar Allah da ta hanyar samun yardar mijinta. 

Lokaci bayan lokaci za ku ji Sarkuwata ta tara ‘yan matanta da take shirin ta aurar da su, wadanda babba a cikinsu itace wacce nake son a bani na aura, tana basu labarin cewa; “Yayin da Sayyida Fatima ta yi Shahada, mijinta, Amirulmuminin (AS) ya tsaya a kanta, yana mai cewa; ‘Ya Allah! Ni mai yarda ne da ‘yar Annabinka. Ya Ubangiji, hakika ta sauke min hakkina da ke kanta.” Sai take fadawa ‘ya’yan nata cewa wannan shaidar nake so daga mahaifinku nima, ku dage idan kun yi aure ku kasance masu neman wannan shaidar daga mazajenku.

Hakika na samu ‘yar manyan mutane, ‘yar mutunci da arziki. Ba fa arzikin kudi ba, domin kuwa Mahaifin nata ba shi da wani tarin abin Duniya, face dai Allah ya masa rufin asiri. Wannan ne ma yasa take yawan cemin, ta amince na aureta da rufin asiri na, in Allah ya nufi mu yi dukiya Shi ya so. Idan bai nufa ba kuwa arzikin da ya mana abin godewa ne. 



Ina tsananin kaunar wannan budurwar tawa saboda na taba tambayarta a wani lokaci muna ‘chat’, nace mata mene ne labari? Sai ta bani labarin wata mata da tazo tana tambayar Annabi (S) akan hakkokin miji da ke kan matarsa, sai yake ce mata: “Ta biya masa bukatarsa ko da tana cikin uzuri (lokacin da ya neman), kuma kar ta gabatar da wani abu face da izininsa, idan ta aikata ba tare da amincewarsa ba tana da dakon aikin, shi kuma yana da ladansa (aikin da ta yin mai kyau), kuma kar ta yi bacci da daddare matukar yana mai fushi da ita.” A lokacin sai take cemin, “Ina son ka zama miji na, Allah ya bani ikon sauke dukkan hakkokinka da ke kaina ko na samu kyakkyawar sakamako a wajen Allah, Ya kai Uban ‘ya’yana.”

Na sha fada mata wani Hadisin Annabi (S) da yake cewa: “Duk wanda ya ke da wata mace wacce ta ke cutar da shi, Allah ba zai karbi sallarta ba, ba kuma zai karbi duk wani kyakkyawa daga ayyukanta ba ko da ta kare zamani tana azumi, har sai ta samu yardar mijinta.” Nake cewa, bani fatan ki kasance a sahun irin wadannan matan Ya ke matar aurena.

Ya ke abar kaunata, na roke ki da ki kasance min mafi alkairin jin dadi a rayuwata. Domin na ji a hadisi Manzon Allah (S) yana cewa: “Mafi alkairin jin dadin duniya shine samun mace tagari.” Na yi miki alkawarin sauke duk hakkokinki da ke kaina bayan aurenmu gwargwadon iyawata, na daga kosar da dukkan nau’in yunwarki, tufatar da ke, ilmantarwa da kuma biyan bukatunki. Ko ba komai naga wani hadisi a cikin ‘Mizanul Hikma’ daga Manzon Allah (S) yana cewa: “Hakkin mace ne akan mijinta ya kosar mata da yunwarta, ya suturce mata al’auranta.”

Zan kuma yi kokarin zama a gareki kamar yadda Annabi (S) yake cewa: “Mafiya alkairin mutane daga cikin al’ummata sune wadanda ba su tsawwalawa iyalansu, kuma ba su zaluntarsu.” Zan yi matukar burin na tsinci kaina daga cikin wadanda Annabi (S) yake cewa: “Babu wani bawa da zai fita ya nemo abinci, sannan ya zo ya ciyar da iyalansa, face Allah ya ribanya masa a kan dukkan dirhami daya da ya ciyar da su zuwa dirhami dari bakwai.”

Ya ke abar kaunata, ina mai alfahari da zamarki Budurwata. Zan ji dadi fiye da na yanzu bayan an daura aurenmu. Fatanmu shine Allah ya bamu zuriya masu albarka, tsayayyu a tafarkin Allah, masu sallamawa ga Jagora, wakilai na gari ga addinin Allah da sakonSa.

Tunatarwa ce kawai... 

 - Saifullahi M. Kabir
 10/10/2016 
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post