...Umar Hassan Gololo...
Da aka ce wai an tarewa General Buratai hanya,wadansu kuma suka ce anyi yunkurin hallaka shi,sai 'Yan-jarida suka tambayi Mai magana da yawun rundunar Sojojin Nigeria na wancan lokacin Brigadier Sani Usman Kukasheka cewa to yanzu a wane hali Chief Of Army Staff yake.? Sai yace an kashe dukkan wadanda suka tare hanyar ko suka yi yunkurin hallaka shi,yanzu haka ma yana can suna ganawa da Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris.
An tare hanya an kuma kashe wadanda suka tare hanya,to me ya rage kuma.?
Sai a dauki gawarwakin ayi binciken su wanene.? Kuma wanene ya turo su.?
Wannan bai samu ba sai rundunar Sojojin Nigeria karkashin wannan jabberin Buratai ta dumfari gidan Malam Zakzaky(H) ta kwashe kwanaki biyu tana ruwan wuta akan wadanda basu da makamai suka yi kisan da wani Soja yace sun yi amfani da Makaman da ko a yaki da Boko-Haram ba a basu irinsu ba,laifinsu shine ana zargin 'yan-uwansu da tare hanya wa Buratai.
Mutane sun yi mamaki da al'ajabin irin wannan ta'addancin.
Kwatsam sai ga Yarima Muhammad Bin Salman yana cewa sune suka dauki nauyin wannan ta'addancin domin wai su rage tasirin Iran a Nigeria.
Wannan maganar ta Yarima tun daga kan Shugaban Nigeria har karnukansa da ake kira Malamai babu wanda ya musanta,kenan dama kisan kiyashin Zaria tsararren al'amari ne.
Anyi amfani da karfin soja domin rusa da'awar Malam Zakzaky(H) amma an kasa amfani da irin wannan karfin domin samar da tsaro a Jihohin Arewa maso Gabashi da Yammacin Nigeria..
Zalunci ko Adalci.......???