Takaitaccen Tarihin Sabon Sarkin Zazzau, Mai Martaba Ahmed Bamalli
Daga Bangis Yakawada
Mai Martaba Ahmed Bamalli shine tsohon jakadan Nijeriya a kasar Thailand, inda ya sauka yanzu aka saka wani kuma ake shirin mayar da shi kasar Myanmar.
An haifeshi a ranar 8 ga watan Yunu, 1966.
Yayi digiri da digirin digirgir a fannin International Relations and Diplomacy daga jami'ar ABU Zaria da jami'ar jihar Enugu da jami'ar York da jami'ar Oxford. Sannan a 2011 yayi wani kos a fannin sha'anin gudanarwar Gwamnati a jami'ar Harvard.
A yanzu shi ke rike da mukamin Magajin Garin Zazzau, sarautar da mahaifinshi ya taba rikewa.
Mai Martaba Bamalli ya rike Darakta a Bankin FSB International Bank a 1998, ya kuma yi manaja a hukumar Abuja Metropolitan Management Authority a 2006.
Daga bisani ya sauya aiki zuwa kamfanin sadarwa na Nigerian Mobile Telecommunications Limited (MTEL). Daga bisani ya koma Darakta a ma'aikatar buga kudi da tsaro wato Nigerian Security Printing and Minting Plc.
Bayan sauya Gwamnati a Kaduna a 2015, Gwamna El-Rufai ya nada shi Kwamishina a hukumar zabe ta jihar Kaduna. A 2017 El-Rufai ya aika sunan Bamalli a jerin wadanda Buhari zai nada jakadun Nijeriya a kasashen waje.