Ta'addancin Gwamnatin Buhari A Zariya, A Shekara Ta 2015


 

@Isma'il Abubakar Idris Katsina.


A yau shekara Biyar 5 dai-dai da ta'addancin gwamnatin buhari ga 'yan shi'a da Malaminsu Malam Ibrahim Zakzaky da fakewa akan cewar wai! SuntarewaHamshakin Sodiji Yusuf Tukur burtai hanya asali ma burtai baya garin yana yankin mai duguri a ranar.


Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari yayi dauki albashin kawar da Shi'a da 'yan Shi'a a doron Kasarmu ta Najeriya sai gashi wankin hula ya kaisu tare, abinda kowa yasani ne a dukkan inda 'yan shi'a suke basa tare hanya sunada masu Traffic a gabansu da gefe da baya domin gujewa Hatsari a dukkan inda suke tarukansu na yau da kullin.


Sai gashi Buhari ya tura Sodoji a Wajen taron 'yan Shi'a wato Hussainiyya Baqiyyatullah sunyi abinda sukaga dama da sunan tare anya a matsayin ka na mutum ba dabba ba! Dama kisan mutane sama da 2,000 da raunatasama da 1,000 ne hukuncin tare hanya, idan hakane tsare malaminsu Malam Zakzaky wanda kowa yasanshi dason zaman lafiya tsareshi shekara biya 5 duk cikin hukuncin tare hanya ne..?


Idan antarewa Shugaban Sodoji hanya miyakai Sodoji a Gyalesu gidan Malam Zakzaky suka farmasa suka kashe masa mabiya dubinnai da yaransa na cikinsa tare ba shafe gidansa ya koma Fili, bayan kunnawa gidan malam wuta da jefa burneti, Sodoji sun kashe malam amma Allah ya tadashi sun jashi kasa jini na kwarara a jikinsa, sun harbi matar malam Malama Zinatu.


Miyakai Sodoji a Fodiyya Center dan magaji canma hanyar aka tare zatakai su rusata an mai data fili ga Makabartar Shaidai Darurrahama canma sunje sun tone kabarin shahidai duk wannan tare hanya ne.


Sunyi rami a Makabartar Mando Last sun buzne Maza da Mata, Yara da Manya, wasu daransu basu mutuba akayimasu kudin goro aka buzne rami daya wannan Zalunci ko zamanin fir'auna ba'ayi kwatan kwacinsa ba!.


Idan hukuncin kisa ne ga masu tare hanya buhari da sauran 'yan siyasa a kamata a kashesu domin wajen kamfe suna tare hanya, masallatan juma'a da coci ana tare hanya, ga masu zanga-zangar Sars da masu Zanga-zanga akan barazanar tsaro a Arewa miyasa ba'a farmasu ba..?


Idan maiji magana wawane baikamata maiji ya zama wawa kalarsa ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post