Su Waye Suke Bayyana A Tituna Kulli Yaumin A Abuja??


 

Khadija lawan daura ✍️


Da sunan Allah Mae kawar da Azzalumae.


Suwaye wannan mutanen da suke futa kan titina kullum suna wasu waqe ?


Kuma waqen meye sukeyi?


Sannan meye dalilin futowar?


Sudin wasu tsurarun matasa ne, Wanda baifi a tsaya aji meye damuwansu ba.


Sannan dalilin futowar su shine.


Kamun malaminsu shaikh zakxaky da kashe musu yayu da kanne da iyaye da Abokae a wata rana da muke Kira 12 December 2015.


Dalilin kama malaminsu shaikh zakxaky yasa duk suka tare a birnin tarayya Abuja Dan nunama gwamnatin Nigeria kin aminchewa da kamun malaminsu,

Amma wannan bae Hana gwamnatin Nigeria ta dirar musu ba a matsayin su na Yan kasa Kuma Wanda ake chemusu suma sunada yanchi,

Sunyi zanga-zangar lumana Kai har a human rights da babban sakateriya na kasa an shekar da jinin musulmae almajiran malan zakxaky, bakuma da sunan an gama bane yanxu haka babu babban burin gwamnatin Nigeria daya wuche ta farwa wannan matasan na garin Abuja masu Neman yanchin jagoransu . 


Amma babban kuskuren da kukayi shine sudin an tarbiyantar dasu akan chewa shifa wanna addini Dole zaka iya gamuwa da Abu biyu kisa ko dauri dan haka wanna baya tsorasu Kuma kisa sun San chewa shahada ne dauri Kuma sun San chewa makarantar Annabi Yusuf che su futo su dada daga inda aka tsaya 


Babban Abunda yake sani kuka da baqin chiki wadanda suke kashe wannan raunana matasan da wuya kagansu matasa dukkan su sa'annin iyayenmu ne Basu tuna yanda suke San yaransu suma wannan matasan iyayensu suna sansu .


Sannan Basu tuna chewa suma haefarsu akayi sunada galihu Kuma sunada yanchi Amma yanchin ba a gurin shuwagabannin Nigeria ba a wurin Allah ta'ala ne sukeda yanchi 


#FREEZAKZAKY

#FREEUMMAZEENA

#NOTOINJUSTICE

#FREEDOM FOR ZAKXAKY.


Wasallahu Ala Muhammad wa Alihi dayyibinad-dahirin

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post