Wasa wasa abu yana neman zama mummuna, an fara zanga zanga da sunan rusa sashen yaki da yan ta'adda da masu miyagun laifuka, 'SAR' duk da an kafa Wannan sashe bisa ka'ida Amman aka amince da bukatar masu zanga zangar wajan biya musu bukata.
Abin mamaki maimakon zanga zanga ta tsaya sai abin ya dauki sabon salo, inda ya koma kamar kabilanci ana kokarin sauke gwamnati ta karfin tsiya. Kuma wasu kabilu ne sukafi nuna Wannan mummunar manufa.
Abin tambaya shin wai ina shugaba buhari yake ne da ya Bari abin nan yake kara muni yayi gum da bakinsa ko so Ya ke tarihi Ya maimaita kansa abin da akayi masa a 1985 yasake afkuwa?
Yakamata masu zanga zanga su fahimci cewa Wannan gwamnati fa zababbiyace Don haka kada suyi tunanin zasuci nasara irin yadda akayi a kasashen afirika, inda shugabanin wadancan kasashe suka zama na dindindin. Turawa basa goyon bayan rusa damokoradiyya musamman Wadda akayi zabe.
Lalle yakamata buhari ka farka daga dogon barcin nan da kakeyi katashi tsaye kacimma makiyan ka makiyan kasar nan kafin su cimmaka su cimmana.
Musa Ibrahim Daura
20-10-2020