Shin, Wa Ya Kamata A Kira Shi Malami???


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BA KOWANNE MAI KARATU AKE KIRA MALAMI BA 

Da yawan mutane basu san wa ake kira malami ba, saboda haka kake gani suna bin jahilai da batattu a matsayin malamai jagorori. 

Dangane da fadin Allah (T) cewa; 

 " إِنَّما يَخْشَى اللَّهَ مِنْ عِبادِهِ الْعُلَماءُ ."

" ABIN SANI KAWAI MASU TSORON ALLAH DAGA BAYINSA SUNE MALAMAI ."

Imam Ja'afar As-Saadiq (A. S) yace; 

قَالَ يَعْنِي مَنْ يُصَدِّقُ قَوْلَهُ فِعْلُهُ وَ مَنْ لَمْ يُصَدِّقْ قَوْلَهُ فِعْلُهُ فَلَيْسَ بِعَالِمٍ.

" ANA NUFIN WANDA AYYUKANSA KE GASKATA MAGANARSA NE, AMMA WANDA AYYUKANSA BA SA GASKATA MAGANARSA BAI KASANCE MALAMI BA ."

Tunda kuwa hakane za mu iya cewa ashe yawancin masu daura dankwali a kansu ba malamai bane komai yawan karatunsu. 

Dalili kuwa shine, Idan ka saurari maganganunsa sannan ka auna su da ayyukansu sai kaga wannan yayi gabas ne yayin da wannan yayi yamma. Kenan ba sune masu tsoron Allah ba, kuma duk wanda ya bi su za su kai shi ga halaka. 

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏2، ص: 59

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

Tare da Ado Isah Guda. 

11th Oct, 2020/ 24th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post