SHIN MU BA ƳAN ƘASA BANE: Fiye da awanni arba'in da takwas (wanaki biyu) miyagun sojojin Najeriya su ɗauka suna kashe almajiran Shaikh Zakzaky a tsakanin Husainiyyah Da Gidan Malam



Fiye da awanni arba'in da takwas (wanaki biyu) miyagun sojojin Najeriya su ɗauka suna kashe almajiran Shaikh Zakzaky a tsakanin Husainiyyah (wurin gabatar da tarurrukan almajiran Shaikh Zakzaky) da Gyallesu (gidan Shaikh Zakzaky) inda suka kashe fiye da mutane dubu 1000+ wanda su haɗa da mata, maza, manya, yara, tsoffi da masu ciki harda ƴaƴan Shaikh Zakzaky guda uku. Suka bizne fiye da mutane 347 a rami guda, ba tare wanka ba bare sutura kamar yadda addini ya tanadar a matsayinsu na musulmi. Sannan aka raunata da dama daga ciki, hadi da kama wasu adadi masu yawa, sannan suka rushe tare da kona Husainiyyah da gidan Shaikh Zakzaky haɗi da wasu muhallai mallakin almajiran Shaikh Zakzaky, tare da lalata dukiya. Baya ga aiwatar da duk wannan mummunan ta'addancin, daga bisani su kama Shaikh Zakzaky tare da matarsa Malama Zeenah suka tsaresu bisa zalumci, bayan sun aiwatar da mummunan harbi a kansu. Shaikaru biyar kenan zuwa yanzu da aukuwar wannan ta'addancin.


Duk wannan mummunan ta'addancin ya farune bisa umurnin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tare da taimakawar gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nasiru El-Rufa'i. Tsawon wannan lokaci gwamnatin Buhari naci gaba da aiwatar da ta'addanci ga Shaikh Zakzaky da almajiransa. Abin mamakin shine yadda al'umma sukayi tsit da bakinsu akan al'amarin Shaikh Zakzaky, aka bar al'amarin ga almajiransa da danginsa kadai, sai ƴan ƙalilan daga cikin Malaman addini, ƴan siyasa, ma'abota tausayi da kishin Ɗan'adamtaka suke nuna goyon baya da neman ƴanci ga Shaikh ɗin da Almajiransa.


Kalli yadda al'umma suka yi caaa....! Akan Buhari dangane da kisan da sojoji sukayi wa masu zanga-zangar #EndSars a birnin Legas dake kudancin Najeriya, ƴan awanni da faruwar hakan amma duniya da ɗauka ta kowace kusurwa ana Allah-wadai da gwamnatin Buhari. Mutanen da sojoji suka kashe a Legas basu kai kashi ɗaya cikin goman almajiran Shaikh Zakzaky da sojoji suka kashe a Zaria ba. Dukda mummunan martani da matasan suka mayar na ƙona wurare masu muhimmanci mallakin gwamnati, tare da asarantar da dukiya da kashe wasu daga cikin jami'an tsaron da suka aiwatar da kisan ƴan uwan nasu a Legas, amma dukda haka al'umma ta kowace ɓangare a sassan duniya suna muzanta Buhari akan wannan ta'addanci, ciki kuwa harda masu tunanin saukar Buhari daga kan kujerar shugabancin Najeriya shine abinda ya dace da Buhari bisa wannan mummunan aiki nasa.


Tambayar da take buƙatar amsa ga kowane ma'abocin lafiyayyen hankali shine, mai yasa mu almajiran Shaikh Zakzaky bamu samu wannan gatan daga al'umma ba? Meye laifin mu, Meye bambamcinmu da matasan da aka kashe a Legas ta fuskacin zama ƴan ƙasa ? wace doka mu karya ta Shari'a, al'ada ko ta tsarin mulkin ƙasa da mu cancanci ayi mana wannan mummunan kyarar a matsayin mu na ƴan Najeriya? idan har akwai gamsassun amsoshin waɗannan tambayoyin to muna buƙata. Idan kuwa babu to ya tabbata kisan kiyashin Zaria shiri ne na Buhari dana wasu masu gidansa na ciki da wajen ƙasar domin cimma wata mummunar manufa tasu.


Mu bama goyon bayan kisan zalumcin da gwamnati ke yiwa ƴan kasa koma daga wane bangare ne ko yare (Musulmi ko Kirista, ɗan Arewa ko ɗan Kudu). Mu abinda muke cewa shine: Bama goyon bayan zalumci ko a kan waye. Shi rai, rai ne, sabida haka hatta dabba bama goyon bayan kashe sa idan har bada hakki na Shari'a ba. Babu la'akari da Addini, Kabila, Yare, Launi ko Fahimta wajan tabbatar da adalci. Mu dukaninmu ƴan ƙasa ne masu cikakken ƴanci, sabida haka ayiwa kowa adalci.


– Abbakar Ibraheem Kudan.

   22102020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post