GA AMSA NAN CIKIN SAHIHUL BUKHARI
Sau da yawa za kaji wasu na cewa gaskiyar magana an sami wasu mutane da dama wadanda suka canza daga abinda Annabi Muhammad (S. A. W. W) ya barsu a kansa a bayansa, sai kuma wasu na qayyatawa, wasu kuma na jingina wannan furuci ne ga mabiya mazhabar Ahlul-Bait (A. S) wanda aka fi sanin su da 'yan Shi'ah.
Wasu kuma na cewa a'a , wannan magana nanan cikin dukkan littafan musulmi Sunnah da Shi'ah. To, yanzu sai za mu leqa ne cikin mafi girman littafin sunnah muga abinda yazo daga cikinsa.
Ga shi kamar haka;
6643 - حدثنا يحيى بن بكير: حدثنا يعقوب بن عبد الرحمن، عن أبي حازم قال: سمعت سهل بن سعد يقول:
سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: (أنا فرطكم على الحوض، من ورده شرب منه، ومن شرب منه لم يظمأ بعده أبداً، ليردنَّ عليَّ أقوام أعرفهم ويعرفونني، ثم يحال بيني وبينهم) قال أبو حازم: فسمعني النعمان بن أبي عياش وأنا أحدِّثهم هذا، فقال: هكذا سمعت سهلاً؟ فقلت: نعم، قال: وأنا أشهد على أبي سعيد الخدري لسمعته يزيد فيه قال: (إنهم مني، فيقال: إنك لا تدري ما بدَّلوا بعدك، فأقول: سحقاً سحقاً لمن بدَّل بعدي) [ر:6212
Yahya Bn Bukhari ya bamu labari, Ya'aqub Bn Abdurrahman ya bamu labari, daga baban Haazem yace, na ji Sahal Bn Sa'eed yana cewa, na ji Annabi (S. A. W. W) yana cewa;
" NI MAI BARINKU NE AKAN TAFKINA, WANDA YAZO MASA YASHA DAGA GARE SHI, KUMA WANDA YASHA DAGA GARE SHI BA ZAI TABA JIN QISHI BA A BAYANSA HAR ABADA !
ZA AZO MIN DA WASU MUTANE, ZAN GANE SU (wane-da-wane ne da kuma wane),KUMA SUMA ZA SU GANE NI, SA'ANNAN A SHIGA TSAKANINA DA TSAKANINSU ( ta yadda ba za mu hadu har muyi musafaha ba) ."
Abu Haazem yace, Nu'uman Bn Abiy Iyaash ya ji ni ina ba su wannan labari sai yace, (da gaske) haka ka ji Sahal ke fada ? Nace eh (tabbas haka naji daga bakinsa). Yace, nima na kasance tare da Abu Sa'idul-Khudriy kuma na ji shi yana qari cikinsa (da wannan kalma)
" SU FA (mutanen nan) DAGA GARE NI SUKE (mun zauna tare kuma sun bi ni lokacin ina raye har na bar cikinsu) ."
Sai ace, " Ai kai baka san abinda suka canza a bayanka ba ."
" SAI NACE, NESA NESA GA WANDA YA CANZA A BAYANA !"
Hadisi mai lamba (6212).
To, yanzu laifin na waye, Shi'ah ko Sunnah?
Ko kuma dai dukka ne?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
30th Sep, 2020/ 13th Safar, 1442.
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com