Shekaru Biyu Da Kashe Yan Uwa Almajiran Sheikh Zakzaky 49 A Garin Abuja



 A lissafin watannin Miladiyya yau muna ranar 29/10/2020 yayi dai-dai da shekaru biyu da Sojojin Najeriya suka afkawa yan uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) masu Tattakin Yaumu Arba'in na Imam Hussain a garin Abuja.


 Duk da muna wata ne na Mauludin Fiyayyen halitta hakan bazai sa mu manta da irin ta'addancin da Azzaluman gwamnatin Najeriya ta aiwatar mana a irin wannan rana, sun kashe mana yan uwa Hazikai sama da 49 tare da jikkata 200 duk a wannan rana, wanda har yanzu wasu suna jinya basu warke ba.


 Laifin wannan mutane da aka kashe mana tun daga ranar 27, 28 zuwa 29 shine kawai sun fito gabatar da Muzahara na tunawa da kwanaki 40 na Shahadar Imam Hussaini ba tare da sun fasa ko lalata kayan wani ba tafiya kawai suke akan titi basa cutar da kowa. Allah ya dauka mana fansar jinin yan uwamu da aka kashe ya saka mana da wannan zalunci da gwamnatin Buhari ta aiwatar mana.


 - Ibrahim Almustapha Saminaka

 - 29/October/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post