Shahadar Manzon Allah (S) Tazo Da Wasu Abubuwan Ababen Nazari 😭😭😭😭




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MAGANI MUKA 'DURA MASA IN JI UMMUL-MUMININA A'ISHA 


Fadin Allah (T) cewa kowacce rai mai dandana mutuwa ce, koma komai na da qaddara (sanadi). 


Yau ashirin da takwas (28) ga watan Safar shine yazo daidai da ranar shahadar fiyayyen halitta Manzo Muhammad Bn Abdullahi (S.A.W.W) wanda yayi a shekara da goma sha uku (13) bayan hijra. 


Bayan dawowarsa daga aikin Hajjinsa na bankwana ya kwanta jinya wacce a cikinta ya koma ga mahalicinsa. 


Sai dai cikin wannan jinyar tasa ce akayi amfani da wata dama aka dura masa guba (poison) wanda hakan yayi sanadin wafatinsa. 


Na'am, wannan al'amari bai zama abin mamaki ba, domin hakan ne zai qara masa wata jaraja kan wacce yake da ita. Mutuwar shahada ita ce mutuwa mafi daukaka wacce take qara daukaka darajar mutum zuwa wani matsayi wanda Allah ne kadai ya sani. 


Daga bakinsa mai albarka (S. A. W. W) muka ji wannan matsayi na shahada, saboda haka Allah ya qara daukaka matsayinsa da wannan daraja ta shahada. 


Don gudun tsawaitawa za mu taka birki anan mu koma cikin riwayar da Bukhari ya kawo daga Ummul-muminina A'isha cikin sahihinsa. 


Ga riwayar kamar haka 


πŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌπŸ‘‡πŸΌ


5382 - Ψ­Ψ―Ψ«Ω†Ψ§ ΨΉΩ„ΩŠ Ψ¨Ω† ΨΉΨ¨Ψ― Ψ§Ω„Ω„Ω‡: Ψ­Ψ―Ψ«Ω†Ψ§ ΩŠΨ­ΩŠΩ‰ Ψ¨Ω† سعيد: Ψ­Ψ―Ψ«Ω†Ψ§ Ψ³ΩΩŠΨ§Ω† Ω‚Ψ§Ω„: Ψ­Ψ―Ψ«Ω†ΩŠ Ω…ΩˆΨ³Ω‰ Ψ¨Ω† أبي ΨΉΨ§Ψ¦Ψ΄Ψ©، ΨΉΩ† عبيد Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ¨Ω† ΨΉΨ¨Ψ― Ψ§Ω„Ω„Ω‡، ΨΉΩ† Ψ§Ψ¨Ω† ΨΉΨ¨Ψ§Ψ³ وعائشة: 

Ψ£Ω† Ψ£Ψ¨Ψ§ Ψ¨ΩƒΨ± رآي Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ†Ω‡ Ω‚Ψ¨َّΩ„ Ψ§Ω„Ω†Ψ¨ΩŠ Ψ΅Ω„Ω‰ Ψ§Ω„Ω„Ω‡ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΩˆΨ³Ω„Ω… ΩˆΩ‡Ωˆ Ω…ΩŠِّΨͺ، Ω‚Ψ§Ω„: ΩˆΩ‚Ψ§Ω„Ψͺ ΨΉΨ§Ψ¦Ψ΄Ψ©: Ω„Ψ―Ψ―Ω†Ψ§Ω‡ في Ω…Ψ±ΨΆΩ‡ فجعل يشير Ψ₯Ω„ΩŠΩ†Ψ§: Ψ£Ω† Ω„Ψ§ ΨͺΩ„Ψ―ΩˆΩ†ΩŠ، فقلنا: ΩƒΨ±Ψ§Ω‡ΩŠΨ© Ψ§Ω„Ω…Ψ±ΩŠΨΆ Ω„Ω„Ψ―ΩˆΨ§Ψ‘، فلما أفاق Ω‚Ψ§Ω„: (Ψ£Ω„Ω… Ψ£Ω†Ω‡ΩƒΩ… Ψ£Ω† ΨͺΩ„Ψ―ُّΩˆΩ†ΩŠ) [Ψ±: 4188، 4189]


Aliyu Bn Abdullahi ya bamu labari, Yahya Bn Sa'id ya bamu labari , Safyanu ya bamu labari yace; 


Musa dan baban A'isha ya bani labari daga Ubaidullah Bn Abdullahi , daga Ibn Abbas da A'isha (cewa), 


" Lalle Abubakar ya sumbanci Annabi (S.A.W.W) yana mace. "


 Yace, A'isha tace; 


" Magani muka dura masa a halin rashin lafiyar tasa, shi kuwa yana ta yi mana nuni cewa, 


" KADA FA (ku kuskura) KU 'DURA MIN WANNAN MAGANI !"


Mu kuwa (muka qi) muka ce irin qin maganinnanne fa na marar sa lafiya (duk da cewa ya hane mu). To, a yayin da ya farfado (bayan dura masa maganin nan) sai yace (mana); 


" ASHE BAN HANE KU BA CEWA KADA KUYI MIN WANNAN 'DUREN ?"


NB:- Daga jin wannan magana ta Manzon Allah (S. A. W. W) kowa zai iya fahintar cewa yana magana ne cikin hayyacinsa, shi yasa ma bayan sun qi sun aikata abinda suka yi niyya sai da ya tabbatar masu. 


            TAMBAYA 

          -------------------


Tambayar da za muyi anan ita ce; 


(1)- Shin, menene hukuncin saba umarni ko hani na Manzon Allah (S. A. W. W) ?


" NA RANTSE DA UBANGIJINKA BA ZA SU TABA ZAMA MASU IMANI BA HAR SAI KA KASANCE KAI KAKE YIN HUKUNCI ABINDA YA GUDANA A TSAKANINSU , SA'AN NAN BASU SAMI WANI QUNCI CIKIN ZUKATANSU DAGA HUKUNCIN NAKA BA, SANNAN KUMA SU SALLAMA SALLAMAWA !"


(2)- Shin, me yasa suka qi suka dura masa wannan abinda ya hane su a kansa ?


(3)- Idan aka ce hujjar data kawo hujja ce karbabbiya me yasa ya tabbatar musu da laifinsu? 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

       08126385470


15th October, 2020/ 28th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post