Zanga-zanga hanya ce ta isar da koke ko sako da a ke yi a duk duniya. A kan yi ta ne ta hanyar jerin gwano tare da rera wakoki da kuma daukar kwalaye ko hotuna ma su dauke da rubutu don isar da sakon zanga-zangar.
Mafiya yawan lokacin gwamnati ce abin nufa a zanga-zanga. Salon Zanga-zanga kan iya kasancewa jerin-gwano ko gangami.
A Najeriya ma, a kan yi anfani da zanga-zanga domin samun biyan bukata. To sai dai, dayawan zanga-zangar Najeriya, ta kan koma rikici. Saboda haka, a wurin gwamnati, zanga-zanga tamkar neman kawo rikici ne.
To sai dai, a Najeriya, wanda su ka kebanta da yin jerin-gwano (protest) a cikin ayukkan su, su ne yan Shi'a mabiya Sheikh Ibraheem El-Zakzaky. Tsawon lokaci an san su da yin jerin-gwano a cikin harkokin su; ta kayadaddun ranaku ce duk shekara ko kuma wacce ke tasowa.
Duk da yake dai, jerin-gwanon mabiya Zakzaky kan yawan gamo da farmakin jami'an tsaro, su ne su ka fi kowa fuskantar farmakin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro.
An shaidi jerin-gwanon su da tsari da kiyayewa a duk lokacin da su ka fito. Sabanin abunda ke faruwa a wasu, ba ka taba jin labarin wasu sun yi kutse a cikin jerin-gwanon yan Shi'a da sunan aikata mummuna ba.
A duk tsawon lokaci, ba a taba samun rahoton lalata dukiya ko kaddarori na mutane, ko kuma kai farmaki hatta ko ga wadanda a ke ganin ma abokan adawar su ne. Kullum manufar jerin-gwanon su shi ne sakon da su ke so su isar. Su na da basira, haka kuma tsarin jerin-gwanon su na da kaushi da zafi; kamar yadda wani ka iya cewa. To sai dai, ko makiyin su, zai shaidi tsari da salon lumanar jerin-gwanon su.
A fagen kula da taro da hanya, babu tamkar su. Ko da yake dai su ne da karancin mabiya a cikin yankin, su na da kwarewa da salon kula da taro irin na zamani. Su na da bangare mai kula da hanya da taro tare da samar da tsaro domin hana yin kutse daga waje. Tare su ke tafiya da bangaren ma su kula da hanya, ma'aikatan lafiya da kuma ma su tsaftace muhalli.
Idan dai ba jami'an tsaro sun farmaki taron su ba, to kullum lafiya jerin-gwanon su ke karewa. Hatta idan ma an kai ma su hari ne, to su kan tsayu a kan salon su na lumana ba tare da canzawa ba.
Ko a yayin tunzurawar jami'an tsaro da farmaki, yan Shi'a su kan kasance a salon lumana; sai dai su kan tsayu su dake domin fuskantar yanayin domin neman 'yancin su.
A baya, gwamnatocin Goodluck da Buhari sun afka ma su, inda su ka kashe fiye da 1,000, ciki har da 'yayan Jagoran su shida, amman duk da haka ba a same su da barnata dukiya ko rayuka ba. An harbi shugaban su tare da maidakinsa a yayin harin da a ka kaddamar a gidansa na tsawon kwana biyu, inda daga bisani a ka fice da su a ka tsare ba tare da kyakkyawar kulawar likitoci ba.
Fiye da shekara 5, ana tsare da su ba bisa ka'ida ba tare da cewa kotu ta bada umurnin sakin su. Ba nan kadai ba, mabiyan sa na fuskantar muzgunawa tare da farmaki daga yan sanda a tsawon lokacin, wanda ya hada da hasarar rayuka, kamu tare da tsarewa; ciki har da mata da yara. Duk da wannan kuntatawar, jerin-gwanon da su ke yi a Abuja da sauran jihohi bai canza salo ba daga lumana.
Ina ma a ce ma su zanga-zangar #EndSARS da ma sauran kungiyo za su yi koyi da mabiyan El-Zakzaky. Da hakan ya taimaka wurin tilasta gwamnati wurin yin abinda ya kamata wanda hakan moruwar kowa da kowa ne.
Ya kamata a yaba wa yan Shi'a bisa tsayuwa da jajircewar su sabanin wasu ma su zanga-zangar da ke komawa barnata dukiya da kashe-kashe daga karshe, ko kuma a yi kutse cikin sauki a cikin su domin aiwata barna.
Haka kuma, ya kamata zanga-zanga a Najeriya ta kasance kamar irin ta yan Shi'a. Tsari da Jagorancin 'yan Shi'a shi ne sirrin samun nasarar su tsawon shekaru na gudanar da zanga-zangar lumana.
Ba zai zama illa ba idan ma su shirya zanga-zanga bisa kyakkyawar manufa sun yi koyi da salon mabiya El-Zakzaky na jerin-gwanon lumana. Allah Ya taimaki 'yan Najeriya.
Fassara: Maigari