Sakon Jagora Sayyid Ali Khamene'i (QS) Zuwa Ga Matsan Kasar Faransa !!!


 

SHIN ME YASA YIN SHAKKU KAN KISAN YAHUDAWA YA ZAMA LAIFI A KASAR FARANSA?


​Sakon Jagora Ga Matasan Faransa Dangane Da Cin Zarafin Ma’aiki (SAW)


2020-10-29 10:20:53


Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya aike da wani sako zuwa ga matasan kasar Faransa, dangane da abin da yake faruwa na cin zarafin manzon Allah (SAW) a kasar.


A cikin sakon nasa wanda aka wallafa a shafinsa na twitter, jagora ya ce da matasan kasar Faransa; ku tambayi shugaban kasarku kan cewa, me yasa yin batunci ga manzon Allah ya zama ‘yanci ne a kasar Faransa?

Shin ma’anar ‘yanci ita ce yin batunci da tozarci, musamman ga mutane masu daraja? Shin wannan aikin wawanci bai zama tozarta musulmi da suka kada masa kuri’a ba har ya zama shugaban kasa?

Tambaya ta biyu kuma ita ce; shin me yasa yin shakku kan batun kisan yahudawa a yakin duniya na biyu ya zama laifi, idan ma har wani ya nuna shakku kan faruwar haka a kasar Faransa, to za a daure shi ne a gidan kaso, amma kuma yin batunci da toarci ga manzon Allah (SAW) ya zama ba laifi ba ne, kowa yana da ‘yancin yin hakan?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post