Mlm YaKubu Yahayya Katsina Ya Fadi Gaskiya, Duk Da Wasu Basason Afadi Haka !!

 


GASKIYAR AL'AMARI,


Sanin Mafi Yawa daga Cikin Yan uwane cewa Bayan Waqi'a Malam Yakubu Yahaya Katsina Yayi Kokarin sa  bakin gwargwado don Nusar da Yan Uwa Almajiran Sayyeed Allama Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (h)akan cewa Abinda Yasame mu Jarabawa nee,Kuma Baawa Bai  Gujewa Jarabawar Ubangijin sa,Kamar Yadda Sayyeed Ali Bun Husain Alkhamene'i Yafada Cewa:~


Abinda Yafaru Da Sayyeed Baida makawa,


Sannan Malam Yakubu Yahaya Katsina Yake Cewa:~


Abinda Ya Kamata Yan Uwa Su Dukufa Shine:~


Adduo'i da Gyara Dabi'u(Ruhi)Da Neman Kusanci Zuwa ga Mahalicci Tare da Kyautata Alaqa da Al'ummar Musulmi da muke rayuwa tare,


To Sai Yazama An Ruudi Yan Uwa da cewa Babu Mafita a addu'ar da'ake ko Za'a Cigaba dayi Nan Gaba,


Kuma Hakan Yayi matukar tasiri a Cikin Yan Uwa,ta yadda zakaga ba'awani damuwa da Al'amarin adduo'i da'ake a manya~manyan Garuruwa da kanana ba,Alhaali abinda yafi daacewa Keenan,


Sai Gashi Daliban Dake Karatu @ #Iran Sun Gayyaci Tsohon Wakiilin Jaami'atul Mustapha Dake Kasar Congo{SayyeedZul~Fiqar}Sai Yake Bayyana Cewa:~


Takurar da Yan Uwa Mabiya Mazhabar Ahlulbayt (Shi'a)a Nigeria Suke Fuskanta Zaata Kau,


Amma yanada kyau Suyi Riko Su Lizimci Adduo'i Su Kuma Gyara Dabi'un su(Ruuhi)


Gadai Yadda Shehin Malamin Yayi Jawabi a Kasa a Taron Arba'een da Aka Shirya a Qum{Iran)


 ""Takurar da yan Shi'a a Najeriya suke ciki za ta zo karshe ; su kara jajircewa da addu'o'i da gyaran dabi'u - Inji Sayyid Zulfikar 


A jawabin da ya gabatar, tsohon wakilin Jami'atul Mustapha a kasar Kongo Hujjatul Islam Wal Muslimeen Sayyid Zulfikar ya bayyana cewa, "Irin takurar da 'yan Shi'a a Najeriya suke ciki na zalunci zai zo karshe ne. A kwai bukatar su kara jajircewa da addu'o'i da gyaran dabi'u(Ruhi)".


Sayyid Zulfikar ya bayyana hakan ne a munasabar daren 40 na Imam Hussaini (AS) a Mu'assar Al-Basirah ta 'yan uwa dalibai almajiran Malam Zakzaky wanda suka shirya a birnin Qum da ke kasar Iran a ranar Alhamis din da ta gabata 8/10/2020.


Tun farko, ya fara da nuna girma da fadin wannan munasabar ta 40, da kuma ambato manyan Jakadu da hadiman tafarkin Imam Hussaini (AS) a duniya, kamar su Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a Najeriya.


Ya jajjada cewa, "jajantawa game da munasabar ta 40, ya bayyana munasabar a matsayin wata babbar Silar Ahlul baiyi (AS) da mabiyan su".


Sayyid Zulfiqar ya yi kira ga 'yan uwa daliban da sauran 'yan Shi'a almajiran Allamah Sayyid Zakzaky (H) da su yi riko da Al-Qur'ani; koyon karatun sa; yawan karanta shi da aiki da shi; kamar yadda Sayyid Zakzaky (H) a lokacin da ya gana da Imam Khomainy (QS) a ganasawarsa ta farko a rayuwarshi jim kadan bayan juyi, ya bashi Al-Qur'ani, ya ce masa, "Kaima kaje ka kira al'ummar ka a kan dabbaka koyarwar Al-Qur'anin nan".


Sayyid ya ambata cewa, "Zalunci da takurama mabiya Ahlul baity (AS) a Najeriya ko shakka babu zai kawo karshe, amma fa hakan na da bukatar jajircewa da dakewa a kan tafarkin Wilaya da dawwama a kan addu'o'i da siffantuwa da dabi'un addini".


Daga karshe ya yi ishara da yin riko da addu'o'in Sahifa Sajjadiyyah ta Imam Aliy Zainul Abideen (AS).

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post