BIDI'ANTAR DA MAULIDI SABODA SAHABBAI BASU YI BA; TSINTSAR JAHILTAR HUKUNCE-HUKUNCEN SHARIA NE, DON BABU WATA AYAR QUR'ANI KO INGANTACCEN HADISI DA YA CE; SAI SAHABBAI SUN AIKATA WANI AIKI; SANNAN AIKIN YA SAMU GURBI A MUSULUNCI. HASALIMA AIKIN SAHABBAI BAI CIKIN MASDARORIN SHARIA (SOURCES OF SHARI'A). QUR'ANI DA INGANTATTUN HADISAI NE MASDARORIN SHARIA:
Ibn Taimiyya ya na cewa:
"Ibadah ta kunshi dukkan wani abu da Allah ya ke so a aikata ko a fada" (Duk wani abu da mutum zai aikata; Ibadah ce, mutukar babu nassin akan haramcin sa ko karhancin sa. Haka zalika nisantar haramci da karhanci Ibadah ne. Kadan daga cikin misalan Ibadah shine) son Allah da Annabi(saw)...:
يقول ابن تيمية في رسالته "العبودية": "العبادة هي اسم جامع لكل ما يحبه الله ويرضاه من الأقوال والأعمال... حب الله ورسوله... (رسالة العبودية لابن تيمية، ص 38).
Ibadah ita ce dukkan wani aiki mai kyau da Allah ya ke so, kuma babu inda Allah ya haramta shi. Ibadah ta kunshi raya alamomin (sha'a'ir na) Addini:
العبادة: تشمل كل الأعمال الصالحة التي يحبها الله وترضيه. العِبَادَةُ: الشعائر الدينيَّةُ. (معجم الوسيط). العِبَادَةُ: إقامة الشعائر الدينية. (معجم الرائد).
Atakaice, idan an ce Ibadah ba kawai ana nufin Wajibi ba. Hukunce-hukuncen Ibadah sun kunshi: Wajibi, Mustahabbi, Halal, Haram da Makaruhi.
Allah(swt) ya na cewa:
قُلۡ بِفَضۡلِ ٱللَّهِ وَبِرَحۡمَتِهِۦ فَبِذَٰلِكَ فَلۡيَفۡرَحُواْ هُوَ خَيۡرٞ مِّمَّا يَجۡمَعُونَ. (ﻳﻮﻧﺲ : 58).
"Ka ce, saboda falalar Allah(swt) da rahamarsa; su yi farin-ciki (murna), irin wannan (taron na murna akan falalar Allah da rahamasa) ya fi ko wane taro alkhairi".
A wannan ayar, Allah(swt) ya na umartar mu da yin farin-ciki da murna akan falalarsa da rahamarsa.
Akwai wata rahamar Allah da takai Annabi Muhammad(saw)???
Allah(swt) ya tabbatar mana da cewa; Annabi Muhammad(saw) rahama ne ga dukkan Talikai (duk wani abinda ba Allah(swt):
ﻭﻣﺎ ﺃﺭﺳﻠﻨﺎﻙ ﺇﻻ ﺭﺣﻤﺔ ﻟﻠﻌﺎﻟﻤﻴﻦ. (ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ : 107)
Abdullah Ibn Abbas (daya daga cikin manyan Sahabbai kuma masanan Tafsiri) ya na cewa:
ﻓﻀﻞ ﺍﻟﻠﻪ : ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻭﺭﺣﻤﺘﻪ : ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص).
"Falalar Allah(swt): shine Ilimi. Rahamar Allah kuwa: ita ce Annabi Muhammad(saw)".
(ﺍﻟﺪﺭ ﺍﻟﻤﻨﺜﻮﺭ ﻟﻠﺤﺎﻓﻆ ﺍﻟﺴﻴﻮﻃﻲ : 4 / 367).
Matukar mutum zai cire son rai, tabbas zai ce; ma'anar Maulidi shine farin-ciki da murna da haihuwar babbar rahamar Allah(swt) ga dukkan Talikai.
Don haka, wannan ya na nuna cewa; taro domin nuna farin-ciki da haihuwar Annabi(saw) aiki ne tabbatacce da nassin Qur'ani.
Allah(swt) ya na cewa:
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ.
"Ni'imar Ubangijinka ka bayyanar da ita (ta hanyar nuna farin-ciki da murna)".
(الضحى : 11).
An ruwaito daga An-Nu'uman ibn Bashir (daga da cikin Sahabbai) ya na cewa, Annabi Muhammad(saw) ya na cewa:
"Bayyanar da ni'imar Allah(swt) alama ce ta godewa (Allah(swt), kin bayyanar (da ni'imar Allah(swt) alama ce ta butulci":
قَالَ عَبْدُ اللَّهِ: حَدَّثَنَا مَنْصُورُ بْنُ أَبِي مُزَاحِمٍ، حَدَّثَنَا أَبُو وَكِيعٍ الْجَرَّاحُ بْنُ مَلِيحٍ، عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ، عَنِالشَّعْبِيِّ، عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ(ص)َ عَلَى الْمِنْبَرِ: "...َالتَّحَدُّثُ بِنِعْمَةِ اللَّهِ شُكْرٌ، وَتَرْكُهَا كُفْر...".
- مسند أحمد | أَوَّلُ مُسْنَدِ الْكُوفِيِّينَ. | حَدِيثُ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ عَنِ النَّبِيِّ(صَ) : الجزء رقم : 30، 32. الصفحة رقم : 95، 96، 390، 392، حديث : 18449، 18450، 19350، 19351...
- ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ : 3943. ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ : 655. ﺷﻜﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻧﻌﻤﻪ ﻟﻠﺨﺮﺍﺋﻄﻲ...
Babu wata ni'ima da Allah(swt) ya yi mana fiye da Annabi Muhammad(saw). Yin Maulidi alama ce ta nuna farin-ciki da bayyanar da ni'imar Allah(swt) ta samuwar Annabi(saw).
Kenan bayyanar da farin-ciki da murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad(saw) Ibadah ce da nassin Qur'ani.
Allah(swt) ya na cewa;
ﺫَٰﻟِﻚَ ﻭَﻣَﻦ ﻳُﻌَﻈِّﻢْ ﺷَﻌَﺎﺋِﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻓَﺈِﻧَّﻬَﺎ ﻣِﻦ ﺗَﻘْﻮَﻯ ﺍﻟْﻘُﻠُﻮﺏِ.
"... Duk wanda ya girmama Sha'a'irillah; tabbas zuciyarsa (cike take) da takawa (imani)"
(ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺤﺞ : ﺁﻳﺔ 32).
Sha'a'irillah shine; duk wani aikin addini da ya ke tunawa mutum girman Allah(swt).
Tabari (babban malamin Ahlus-Sunnah) ya na cewa; Sha'a'irillah shine; abinda ya ke tunawa bayin Allah(swt) (girman) Allah(swt), (wadanda a ke) bautawa Allah(swt) da su (ta hanyar girmamasu):
ﺷﻌﺎﺋﺮ ﺍﻟﻠﻪ: ﻫﻰ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺍﻟﺪﻳﻨﻴﺔ ﺍﻟﻠﺘﻰ ﺗﺎﻛﺪ ﻋﻠﻰ ﻋﻈﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ. قال الطبري: ﺷﻌﺎﺋﺮ ﺍﻟﻠﻪ: ﻫﻲ ﻣﺎ ﺣﻤﻠﻪ (الله) ﺃﻋﻼﻣﺎ ﻟﺨﻠﻘﻪ ﻓﻴﻤﺎ ﺗﻌﺒﺪﻫﻢ ﺑﻪ. (ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺍﻟﻄﺒﺮﻱ : ﺗﻔﺴﻴﺮ ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺤﺞ : ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻓﻲ ﺗﺄﻭﻳﻞ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : ﺫﻟﻚ ﻭﻣﻦ ﻳﻌﻈﻢ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﺍﻟﻠﻪ...).
Annabi Muhammad(saw) ya na cikin Sha'a'irillah, saboda komai nasa ya na tunawa mana girman Allah(swt), hasalima Annabi Muhammad(saw) rahama ne ga dukkan Talikai, don haka yin bukukuwa don nuna so, girmamawa da murna da haihuwar Annabi(saw); alama ce ta imani.
Tabbas, Allah(swt) ya wajabta mana son Annabi(saw) da nassin ayar Qur'ani, don haka Ibn Rajab (babban malamin Ahlus-Sunnah) ya ke tabbatar da cewa son Annabi(saw) rukuni ne daga cikin rukunan addini:
ﻗﺎﻝ ﺍﺑﻦ ﺭﺟﺐ : "ﻣﺤﺒَّﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲ(ص) ﻣﻦ ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ، ﻭﻫﻲ ﻣﻘﺎﺭﻧﺔ ﻟﻤﺤﺒﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ، ﻭﻗﺪ ﻗﺮﻧﻬﺎ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻬﺎ، ﻭﺗﻮﻋﺪ ﻣﻦ ﻗﺪَّﻡ ﻋﻠﻴﻬﻤﺎ ﻣﺤﺒَّﺔ ﺷﻲﺀ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﻮﺭ ﺍﻟﻤﺤﺒَّﺒﺔ ﻃﺒﻌًﺎ ﻣﻦ ﺍﻷﻗﺎﺭﺏ ﻭﺍﻷﻣﻮﺍﻝ ﻭﺍﻷﻭﻃﺎﻥ ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ، ﻓﻘﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ: ﻗُﻞْ ﺇِﻥ ﻛَﺎﻥَ ﺀﺍﺑَﺎﺅُﻛُﻢْ ﻭَﺃَﺑْﻨَﺎﺅُﻛُﻢْ ﻭَﺇِﺧْﻮٰﻧُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﺯْﻭٰﺟُﻜُﻢْ ﻭَﻋَﺸِﻴﺮَﺗُﻜُﻢْ ﻭَﺃَﻣْﻮٰﻝٌ ﭐﻗْﺘَﺮَﻓْﺘُﻤُﻮﻫَﺎ ﻭَﺗِﺠَـٰﺮَﺓٌ ﺗَﺨْﺸَﻮْﻥَ ﻛَﺴَﺎﺩَﻫَﺎ ﻭَﻣَﺴَـٰﻜِﻦُ ﺗَﺮْﺿَﻮْﻧَﻬَﺎ ﺃَﺣَﺐَّ ﺇِﻟَﻴْﻜُﻢْ ﻣّﻦَ ﭐﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟِﻪِ ﻭَﺟِﻬَﺎﺩٍ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻠِﻪِ ﻓَﺘَﺮَﺑَّﺼُﻮﺍْ ﺣَﺘَّﻰٰ ﻳَﺄْﺗِﻰَ ﭐﻟﻠَّﻪُ ﺑِﺄَﻣْﺮِﻩِ.(ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ : 24). (ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ ﻻﺑﻦ ﺭﺟﺐ : 1 / 48).
Idan muna matukar son Annabi Muhammad(saw): me zai hana mu yi murna da farin-ciki da haihuwarsa???
Allah(swt) yana cewa:
...فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِهِۦ وَعَزَّرُوهُ وَنَصَرُوهُ وَٱتَّبَعُواْ ٱلنُّورَ ٱلَّذِيٓ أُنزِلَ مَعَهُۥٓ أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ
"Duk wanda yayi imani da shi (Annabi(saw), ya girmama shi, ya taimakesa, ya bi hasken da aka saukar masa (Qur'ani); to shine mai babban rabo".
(الأعراف : 157).
Mahallus-Shahid din mu shine َعَزَّرُوهُ (girmama Annabi(saw). Wannan ayar tana nuna cewa ya na cikin imani da Annabi(saw) girmamashi(saw).
Babu wani mai musa ko jayayya akan cewa; guraren tarukan Maulidi gurare ne da ake girmama Annabi(saw) da daukaka ambatonsa.
Allah(swt) ne ya fara daukaka ambaton Annabi Muhammad(saw). Allah(swt) ya na cewa:
وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ.
"Mu ne muka (fara) daukaka ambatonka (Annabi(saw)".
(الشرح : 4).
Kenan Allah(swt) ne ya fara Maulidi; tunda Allah(swt) ne ya fara daukaka ambaton Annabi(saw).
Bidi'antar da Maulidi saboda Sahabbai basu yi ba; tsintsar jahiltar hukunce-hukuncen Sharia ne, don babu wata ayar Qur'ani ko ingantaccen Hadisi da ya nuna cewa; sai Sahabbai sun aikata wani aiki; sannan aikin ya samu gurbi a Musulunci. Hasalima aikin Sahabbai bai cikin masdarorin Sharia (Sources of Shari'a). Qur'ani da ingantattun hadisai ne masdarorin Sharia.
Don Allah(swt) ya tabbatar mana da cewa Qur'ani da ingantattun hadisai ne masdarorin Sharia; sai Allah(swt) ya ke cewa:
ﻭَﻣَﺎ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔْﺘُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺤُﻜْﻤُﻪُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ.
"Duk abinda ku ke da sabani akansa, to hukuncinsa ya na ga Allah(swt) (Qur'ani)".
(ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ : 10).
Wannan ayar ta na nuna mana cewa; Qur'ani ne masdarin Sharia na farko.
A wata ayar Allah(swt) ya na cewa:
...ﻓَﺈِﻥ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋْﺘُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺮُﺩُّﻭﻩُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠّﻪِ ﻭَﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝِ ﺇِﻥ ﻛُﻨﺘُﻢْ ﺗُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻵﺧِﺮِ ﺫَﻟِﻚَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻭَﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺗَﺄْﻭِﻳﻼً.
"Idan kuna da sabani akan wani abu; to ku koma zuwaga Allah(swt) (Qur'ani) da Manzo(saw) (inagantattun hadisai), matukar kun yi imani da Allah(swt) da ranar Lahira. (komawa zuwaga Qur'ani da ingantattun Hadisai) ne mafi alkhairi kuma mafi kyaun tawili".
(ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 59).
Imam Ali(as) ya tabbatar da aikin Sahabbai bai cikin masdarin Sharia, wannan ya faru ne a lokacin da Khalifa Umar Ibn Khattab ya kafa 'yan kwamitin Shura, da suka kafawa Imam Ali(as) sharadi akan cewa; idan ya na so su zabe shi khalifan da zai gaji Umar; lalle zai yi khalifanci irin na Khalifa Abubakar da Umar, sai Imam Ali(as) ya ce; zai dai yi khalfanci karkashin koyarwar ayoyin Qur'ani da ingantattun Hadisai. Idan har aikin khalifa Abubakar da Umar ba lalle ya zama; masdarin Sharia ba; to wane Sahabi ne aikinsa zai zama masdarin Sharia???:
ﻭﻟﺬﻟﻚ ﻧﺠﺪ ﺃﻥّ ﻋﻠﻴّﺎً(ع) ﺣﻴﻨﻤﺎ ﻋﺮﺿﻮﺍ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺨﻼﻓﺔ ﻓﻲ ﻗﻀﻴﺔ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺴﺘّﺔ ﺑﺸﺮﻁ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳُﻨّﺔ ﺍﻟﻨﺒﻲّ ﻭﺳﻴﺮﺓ ﺍﻟﺸﻴﺨﻴﻦ، ﺭﻓﺾ ﻋﻠﻲّ(ع) ﺫﻟﻚ ﻭﻟﻢ ﻳﻘﺒﻞ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺇﻻّ ﺑﻜﺘﺎﺏ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳُﻨّﺔ ﻧﺒﻴّﻪ، ﻭﻟﻢ ﻳﺮﺽَ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﺴﻴﺮﺓ ﺍﻟﺸﻴﺨﻴﻦ. (ﺷﺮﺡ ﻧﻬﺞ ﺍﻟﺒﻼﻏﺔ : 1 : 188. ﻗﺼّﺔ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ. ﺍﻟﻤﺤﺼﻮﻝ ﻟﻠﺮﺍﺯﻱ : 6 : 86...).
Don haka, cewa Sahabbai basu yi Maulidi ba; ba hujja ba ce ta haramta Maulidi ba. Idan mutum ya na so ya haramta Maulidi; sai dai ya kawo ayar Qur'ani ko ingantaccen Hadisin da ya hana Maulidi, idan kuma babu, to aja baki ayi shiru.
Mukaddara Annabi Muhammad(saw) da Sahabbai basu yi Maulidi ba, hakan ba ya nuna haramcin Maulidi, saboda an riwaito Annabi Muhammad(saw) ya na cewa:
"Duk wanda ya kirkiro wani abu mai kyau a Musulunci; ya na da ladan (abinda ya kirkiro) da ladan wanda ya yi koyi da shi. Kuma duk wanda ya kirkiro wani abu marar kyau a Musulunci; to ya na da zunubin (abida ya kirkiro) da zunubin wanda yayi koyi dashi akai":
حَدَّثَنِي زُهَيْرُ بْنُ حَرْبٍ، حَدَّثَنَا جَرِيرُ بْنُ عَبْدِ الْحَمِيدِ، عَنِ الْأَعْمَشِ، عَنْ مُوسَى بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ يَزِيدَ، وَأَبِي الضُّحَى، عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ هِلَالٍ الْعَبْسِيِّ، عَنْ جَرِيرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ: ...فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ(ص): "مَنْ سَنَّ فِي الْإِسْلَامِ سُنَّةً حَسَنَةً، فَعُمِلَ بِهَا بَعْدَهُ ؛ كُتِبَ لَهُ مِثْلُ أَجْرِ مَنْ عَمِلَ بِهَا، وَلَا يَنْقُصُ مِنْ أُجُورِهِمْ شَيْءٌ. وَمَنْ سَنَّ فِي الْإِسْلَامِ سُنَّةً سَيِّئَةً، فَعُمِلَ بِهَا بَعْدَهُ؛ كُتِبَ عَلَيْهِ مِثْلُ وِزْرِ مَنْ عَمِلَ بِهَا، وَلَا يَنْقُصُ مِنْ أَوْزَارِهِمْ شَيْءٌ ".
- صحيح مسلم كتاب : العلم | باب : من سن سنة حسنة أو سيئة : (1017 ( 15 )، 1017).
- سنن الترمذي ( 2675 ).
- سنن النسائي ( 2554 ).
- سنن ابن ماجه ( 203 ).
- سنن الدارمي ( 529, 531 ).
- مسند أحمد ( 19156, 19174, 19183, 19200, 19202, 19206 ).
Babban malamin harshen Larabci ﺍﺑﻦ ﻣﻨﻈﻮﺭ ya ce; kalmar ﺳﻦ ta nufin ﺍﺑﺘﺪﺍﺀ ﺍﻟﻌﻤﻞ (kirkira):
ﻓﻘﺪ ﺟﺎﺀ ﻓﻲ ﻟﺴﺎﻥ ﺍﻟﻌﺮﺏ: ﻭﻛﻞ ﻣﻦ ﺍﺑﺘﺪﺃَ ﺃَﻣﺮﺍً ﻋﻤﻞ ﺑﻪ ﻗﻮﻡ ﺑﻌﺪﻩ ﻗﻴﻞ: ﻫﻮ ﺍﻟﺬﻱ ﺳَﻨَّﻪ. (ﻟﺴﺎﻥﺍﻟﻌﺮﺏ : ﺍﺑﻦ ﻣﻨﻈﻮﺭ : ﺣﺮﻑ ﺍﻟﺴﻴﻦ : ﺳﻨﻦ). ﺳﻦ: ﺗﻌﻨﻰ ﺍﺑﺘﺪﺍﺀ ﺍﻟﻌﻤﻞ ﺑﺸﻲﺀ ﻟﻢ ﻳﺴﺒﻖ ﺇﻟﻴﻪ ـ ﺳﻮﺍﺀ ﻛﺎﻥ ﺷﻴﺌﺎ ﻣﺮﺿﻴﺎ ﺃﻡ ﻻ.
Tabbas, babu wani da zai ce Maulidi abu ne marar kyau, don haka koda bayan wafatin Annabi(saw) da Sahabbai aka kirkireshi; to Allah(swt) ya na bada lada ga wanda ya kirkireshi da wanda ya yi koyi da shi.
Ibn Taimiyya ya na cewa:
ﻭﺃﻣﺎ ﻣﻦ ﺍﺑﺘﺪﺃ ﻓﻌﻞ ﺷﻲﺀ ﻭﻟﻢ ﻳﺴﺘﻨﺪ ﻓﻴﻪ ﺇﻟﻰ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ ﻣﻌﺘﺒﺮ، ﻓﻬﻮ ﻣﺒﺘﺪﻉ.
"Dan bidi'a shine wanda ya kirkiri wani abu da ya kasa kawo dalili na Sharia (Qur'ani ko ingantaccen Hadisi) akai".
(ﺍﻟﻔﺘﻮﻯ ﺭﻗﻢ : 32897).
Kenan Ibn Taimiyya yana nufin; duk wani abinda aka kirkiro matukar akwai madogara daga ayar Qur'ani ko Ingantaccen Hadisi, to ba bidi'a ba ne.
Tunda ayoyin Qur'ani da ingantattun hadisai sun tabbatar da halaccin taro Maulidi, cewa Sahabbai basu yi ba; ba ya zama hujja ta haramtashi.
Allah(swt) da Annabi Muhammad(saw) ne su ke da hakkin halastawa ko haramtawa.
Tambayoyin da masu bidi'antar da Maulidi su ka kasa amsawa:
1. Sau nawa Annabi Muhammad(saw) yayi wa'azin kasa da Musabaka?
2. Ko zaku iya kawo sunayen Sahabbai 10 wanda suka yi musabaka ko wa'azin kasa?
3. Tsakanin ku da Annabi(saw) da Sahabbai waye yafi son Qur'ani?
4. Idan Manzon Allah(saw) da Sahabbai basu yi musabaka da wa'azin kasa ba; kenan wa'azin kasa da Musabaka bidi'a ne?
5. Idan kuma Annabi(saw) da Sahabbai sun yi musabaka; to a wadanne surori ne Manzon Allah(saw) da Sahabbai suka yi musabaka akansu? A wane gari / wuri ne Sahabbai suka yi wa'azin kasa da musabaka? Ko zaka iya lissafo sunayen abincin da akaci a ranar wa'azin kasa da musabakar Sahabbai?
6. Ko zaku iya kawo aya daya tak ko hadisi akan Falalar Musabaka ko wa'azin kasa?
7. Menene Farillai, sunnoni da mustahabban musabaka da wa'azin kasa?
8. Tunda akwai taruka da bukukuwa da yawa da ake yi wadanda Annabi(saw) da Sahabbai ba su yi ba; me ya sa masu da'awar kauda bidi'a sune kan gaba wajen yinsu?
9. Me ya sa sai biki da taron mauludi ne kadai ya zama bidia?
10. Taya karatun Al-Qur'ani, ciyarwa, cusa kaunar Annabi(saw) suka zama bidi'a?
11. Idan Bidi'a shine abinda Annabi(saw) bai yi ba, to Annabi(saw) ya yi fada da Maulidi? kenan fada ko yakar Maulid shima bidi'a ne; tunda Annabi(saw) bai taba yakar maulidi ba?
12. Annabi Muhammad(saw) ya taba furta kalmar Ahlus-Sunnah? Akwai kalmar Ahlus-Sunnah a Qur'ani? Wane Sahabi ne ya taba kiran kansa Ahlus-Sunnah? Kenan bidi'a ne wani ya kira kansa Ahlus-Sunnah?
13. Idan kun ce; duk dan bidi'a dan wuta ne, kenan yanzu haka Ibn Taimiyya yana cikin wutar Jahannama? Ina Ibn Taimiyya ya samo asalin raba Tauhidi 3 (Uluhiyya, Rububiyya, As'ma'u was Sifat)?
14. Akwai inda Annabi Muhammad(saw) ya taba raba Tauhidi 3?
15. Ina ne khalifa Abubakar, Umar, Usman, Imam Ali(as) ko wani Sahabi ya taba raba Tauhidi zuwa Uluhiyya, Rububiyya, As'ma'u was Sifat?
16. Wane Tabi'i ne ya taba yiwa Tauhidi irin wannan rabawar da Ibn Taimiyya ya yi?
17. Wane magabaci ne cikin Salaf ko malaman Musulunci da suka gabaci Ibn Taimiyya ya yi irin wannan rabawar ga Tauhidi?
18. Kenan Ibn Taimiyya cikakken dan bidi'a ne; saboda ya kirkiro raba Tauhidi 3; wanda bai da asali daga Annabi(saw) da Sahabbai? Kenan ba masu bikin Maulidi ne kawai 'yan bidi'a ba?
19. Idan 'yan bikin Maulidi 'yan wuta ne; kenan Ibn Taimiyya ya riga 'yan bikin Maulidi shiga wuta?
20. Idan kun ce; Ibn Taimiyya ya samo asalin raba Tauhidi 3 ne daga ayoyin Qur'ani; kenan Ibn Taimiyya yafi Annabi Muhammad(saw), Sahabbai, Tabi'ai... fahimtar ayoyin Qur'ani?
21. Wace ayar Qur'ani ce ko ingantaccen hadisi ya bawa Ibn Taimiyya damar ya kirkiro raba Tauhidi 3, har ya zama addini; har ma ake kafirta wanda bai yi imani da shi ba?
22. Wace aya ce ko ingantaccen hadisin ya ce Ibn Taimiyya ne kawai yake da damar ya mayar da wani abu addin; tare da cewa hakan bai da asali daga Annabi(saw) ko Sahabbai?
23. Idan Ibn Taimiyya yana da damar raba Tauhidi 3 ta hanyar istinbadin wasu ayoyin Qur'ani da Hadisai, kenan masu bikin Maulidi ma zasu iya fito da halaccin Maulidi ta hanyar istinbadin wasu ayoyin Qur'ani da Hadisai? Ko akwai wani nassi da yakebace wannan damar kawai ga Ibn Taimiyya?
24. Shaikh Abubukar Mahamud Gumi, Shaikh Ja'afar Adam Kano... 'yan bidi'a ne? Ina Shaikh Ja'afar Adam Kano ya samo sigar salatin da yake bude karatunsa da shi? Akwai nassi sahihi sarihi akan wannan salatin?
Ga sigar salatin da yake bude karatunsa da shi kamar haka:
والصلاة والسلام على أسعد النبين وأشرف المرسلين نبينا محمد وعلى ءاله وصحبه أجمعين ومن دعوى بدعوته وأسنن بسنته إلى يوم الدين...
25. Idan Maulidi bidi'a ne saboda Annabi Muhammad(saw) da Sahabbai basu yi ba; kenan wannan sigar salatin na Shaikh Ja'afar ma bidi'a ne?
26. Idan Annabi(saw) da Sahabbai basu yi sigar wannan salatin ba; kenan Sheikh Ja'afar Adam Kano cikakken dan bidi'a ne har ya mutu? Ko shi shafaffe ne da mai da zaku manta da irin bidi'ar da yayi? Kenan Ja'afar Adam dan bidi'a ne; tunda wannan salatin da yake bai da asali daga Annabi(saw)?
27. Idan dukkan dan bidi'a dan wuta ne; kenan Shaikh Ja'afar Adam dan wuta ne; tunda har ya mutu yana bidi'a ta hanyar yin sigar salatin da bai da asali?
28. Idan kunce salatin da Ja'afar Adam yake ba bidi'a ba ne; saboda mukaddima (gabatarwa) ce ba salati ba; to Annabi(saw) yayi mukaddima? A ciki akwai wannan sigar da Ja'afar Adam yake? Idan bai ciki, me ya sa Ja'afar ya aje na Annabi(saw) ya kirkiri nasa? Saboda da haka kodai ku kawo inda wannan sigar tazo a ruwaya ko ku yarda malaminku dan bidi'a ne? Cewa Wannan sigar da Shaikh Ja'afar yake ba salati ba ne, ba haka ba ne, salati duk inda aka ma Annabi(saw) salati sunansa salati ko a khuduba ko a mukaddima! Ko kuna so ku ce ba'a samu ladan salati idan an yi shi a mukaddima?
29. Ina Shaikh Abubakar Mahamud Gumi ya samo cewa; siyasa tafi Sallah?
30. Ina Allah(swt) ya ce; siyasa tafi Sallah? Akwai hujja daga ingantaccen hadisi da tabbatar da Annabi(saw) ya ce; siyasa tafi Sallah? Wane Sahabi ne ya taba furta hakan?
31. Idan siyasa tafi Sallah; kenan siyasa ibada ce? To Annabi(saw) da Sahabbai sun yi siyasa?
32. Idan babu hujjar da ta tabbatar da cewa siyasa tafi Sallah daga bakin Annabi(saw) da Sahabbai; kenan Shaikh Abubakar Muhamud Gumi dan bidi'a ne???
33. Idan duk dan bidi'a dan Wuta ne; kenan Shaikh Abubakar Mahamud Gumi dan Wuta?
34. Annabi Muhammad(saw) ya taba yin Tafsirin Azumin watan Ramadan?
35. Wane Sahabi ne ya taba ja masa baki???
36. Me ya sa khalifa Umar ya ce; jam'in Sallar Tarawihi (Asham) bidi'a ce???
37. Kenan duk wanda yayi Sallar Tarawihi (Asham) a Jam'i dan bidi'a ne?
38. Idan 'yan Izala suna yakar Maulidi ne; saboda Annabi(saw) da Sahabbai basu yi ba; to me ya sa suke wasu abuwan masu yawa da Annabi(saw) da Sahabbai basu yi ba? Kenan kin Annabi Muhammad(saw) ne ya sa 'yan Izala ke kin Maulidi?
39. Maulidi yana nufin farin-ciki da haihiwar Annabi Muhammad(saw); idan kunce Sahabbai ba su yi maulidi ba, kenan basu yi farin-ciki da haihuwar Annabi(saw) ba?
40. idan har Annabi Muhammad(saw) zai yi koyi da Yahudawa wajen yin Azumin Ashura; to me zai hana Musulmai koyi da Kiristoci wajen yin bikin Maulidi???
➖➖➖➖➖➖➖➖
Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmail.com
🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹🌈🌹