Masu Hankali Zasu Fahimta. FreeZakzaky 5 Years, EndSARS 2 Weeks


 

Yadda za mu kara tabbatar da cewa wasu ke bayan tsare Malam Zakzaky da dirarwa Harkar Musulunci, kuma su ke bayan masu zanga-zangar nan a lokaci guda saboda wani 'interest' dinsu. Su kawai hukumomin kasar nan kayan aikinsu ne.


Ji yadda soji suke kokarin neman a basu dama su kawo karshen zanga-zangar, har da kokarin nuna cewa hakan barazanar kasa ce, kuma su ke da alhakin dakatarwa. Layi 4 Deji ya rubuta ya wa Buratai 'Warning' take fadar shugaban kasa ta tsai da Soji da cewa ba aikinsu bane na yan sanda ne.


Ku dubi yadda su Deji ke wa IG da CPs dinsa kasheji kan duk wanda ya taba su za su kai kararsa a hana shi fita UK, US da sauran kasashen iyayen gidansu, kuma za su maka su a kotun ICC. Nan ma take IGP ya yi maganar jan kunne ga yan sanda kan dirarwa masu zanga-zangar lumana.


#EndSARS kawai suke cewa, an soke SARS din tuni, amma sun baiwa #EndSARS sabbin ma'anoni sun cigaba da shi, har su kan iya tsayar da bangarorin Abuja su yi sanadin mutane su rasa Jirage. A yayin da almajiran Shaikh Zakzaky tsawon shekaru 5 suna cewa #FreeZakzaky ne amma kashe su ake kullum da kamu da dauri.


Ku kalli yadda Osinbajo ke ba masu zanga-zangar #EndSARS hakuri da lallashi, haka ma kwamishinonin yan sanda na lallashi da lalama su, amma ba wani abu tsakanin yan uwa musulmi da gwamnati ko yan sanda ko gwamnati sai bude wuta kawai! 


Abin takaici shine yadda mutanen Arewa, Musulmi, mafi yawa Hausawa duk sanda aka kashe ko aka kama ko aka tarwatsa masu Muzaharar #FreeZakzaky sun samu abin murna ne da tafawa Jami'an tsaro da jinjinawa gwamnati. Alhali duk mai sauran kwakwalwa ya sani Wallahi Tallahi gwamnatin Buhari ba tana tsare da Shaikh Zakzaky ne don shi barazana ne ga kasar nan ba. Kawai suna tsare shi ne saboda shi ma'abocin addini ne, kuma mafita ga Kasar nan.


Saifullahi M. Kabir

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post