Makomar Shugaba Buhari 'Daya Ne Dana Masu Kashe Annabawa (A.S) !!!


 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Idan ka cire yin shirka ga Allah babu laifi mafi girma kamar kashe ran mumini, cikin muminan ma babu kamar Annabawa da A'imma (A. S). 


Babu kokonto kowa ya shaida a tahirin kafuwar wańnan qasa tamu Nigeria ba a taba samun wani dan ta'adda mai gaba da masu yin da'awar yin adalci a doron qasa kamarsa ba. 


Tun yana qaryar cewa shi mai adalci ne kuma wasu wawaye suna gaskata shi kan hakan an wayi gari qananan wawaye sun gane kuskuren su, yanzu manyan daqiqai ne kadai suka rage masu ganinsa a Matsayin adali. 


Babu mai gaba da ayoyin Allah da kuma qaryata su kamarsa, ga kuma goyon baya ga masu tsananin adawa ga Allah (Yahudu da Nasara). 


Wadanda suka gabata basu kashe Annabawa kawai don qiyayyarsu bane, a'a, saboda suna hani ne game da shirka da zumunci, kuma suna umarni da adalci. 


Saurara ku ji abinda Allah (T) ke fada cikin Alqur'ani mai tsarki. 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


إِنَّ ٱلَّذِينَ يَكۡفُرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَيَقۡتُلُونَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَيَقۡتُلُونَ ٱلَّذِينَ يَأۡمُرُونَ بِٱلۡقِسۡطِ مِنَ ٱلنَّاسِ فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ ١٢ 


" LALLE WADANDA KE KAFIRCEWA AYOYIN ALLAH (ta hanyar bijire musu) KUMA SUNA KASHE ANNABAWA BA BISA HAQQI BA, KUMA SUNA KASHE MASU YIN UMARNI DA ADALCI DAGA MUTANE, TO, KUYI MUSU BUSHARA DA (samun) AZABA MAI RADADI (ranar alqiyama). "


To, yanzu me ya bambanta ayyukan Buhari da abinda Allah ke fada cikin wannan aya? 


Allah ya qara da cewa; 


أُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ وَمَا لَهُم مِّن نَّٰصِرِينَ ٢٢


" WADANNAN SUNE WADANDA AYYUKANSU SUKA BACI A DUNIYA DA LAHIRA, KUMA BA SU DA MATAIMAKA (ranar hisabi) . "


(AL-IMARAN, 12-13)


Wadannan ana magana ce kan wadanda suka yi wani aikin kirki ake cewa ayyukansu sun baci. Ina kuma ga Buhari wanda asalan ma bai aikata aikin kirkin ba in ka cire iya ta'addanci da qulla muggan sharruka ga bayin Allah salihai ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

       (08137925034)


21st October, 2020/ 4th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post