Mafita Ba A End Sars Ko End Police Brutality Yake Ba, A End Zalumci Da Azzalumai Take - Inji Umar Hassan Gololo


 

MAFITA BA A ENDSARS KO ENDPOLICEBRUTALITY TAKE BA A END ZALUNCI DA AZZALUMAI TAKE..........!!!

 Mafita Ba A #EndSars Ko #EndPoliceBrutality Yake Ba A End Zalumci Da Azzalumai Take - Inji Umar Hassan Gololo

Wadanda suke cinye kudin albashin 'Yansanda da Sojojin Nigeria suka zamo masu karbar cin hanci da rashawa sune matsalar Nigeria.

Azzaluman da suka cinye kudaden da aka ware domin samar da Ilmi da inganta makarantu sune annoba ga Nigeria da Mutanenta.

Miyagun mutanen da suka sace dukiyar da ya kamata a samar da kwararrun likitoci da Asibitoci a Nigeria sune matsalar al'umma.

Azzaluman da suka sace kudaden gina hanyoyi,suke karbar cin hanci ake shigowa da rubabbun motoci suna kashe jama'a sune matsalar Nigeria.

Babu bala'i ga al'ummar Nigeria kamar barayin da suka sace kudaden samar da wutar lantarki da ruwan sha domin amfanin jama'a.

Ko an ki ko an so sai an fito anyi zanga-zangar kawo karshen zalunci da azzalumai a Nigeria.

Nawa ne albashin Sanata da Dan Majalisar Tarayya dana jiha.? Nawa ne albashin Professor da Kwararren Likita.?

Nawa ne albashin Sojoji da 'Yansandan da suke bamu kariya dare da rana safe da yamma nawa ne albashin Ministoci da Kwamishinonin jihohin Nigeria.?

Zalunci daga tushe ake tumbuke shi ba ganye da reshe ake sarewa ba.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post