Kogin So, Fadawa Ba Wahala, Fitowa Lafiya Sai Mai Sa'a. Kashi Na Hudu (4)


 

Kashi na 4⃣.Rbtw:J. I. R


Bayan su Ahmad sun iso,su tsaya daidai kofar gidan su Zainab.Ahmad ya kira Zainab a waya,don ta fito ta musu jagora zuwa cikin gida,ta kai su masaukin da ta,tanadar,ta zo ta musu sannu cikin fara'a,ta shiga da su.Bayan sun shiga ta sauke su,su dan huta,taje ta kawo musu ruwa mai sanyi,ta kawo abinci da abun sha,da sauransu.Ahmad murna ta sanyasa ya kasa cin komai,se murmushi yake,da kaga fuskansa a wannan lokaci kai kasan farin-ciki ya tafi Ahmad.Nan dai Zainab su gaisa da abokin Ahmad Nura,su ci gaba da yin hira da Ahmad su dade (haduwan masoya da dadi kamar kar arabu).Zainab ta kalli Ahmad ta ce:Ashe dama zan ganka a wanan lokacin Habibi,wlhy zuciya ta yi farin-cikin sanya idanuwata kan naka,Ahmad ya ce:"Uhmmm ai xuciyarki ta so zolayarki ne, domin duk abun da ki bukata daga gareni ki kaddara kin samu.Ba gashi yau gani ga ki ba.My kuma ke ki bukaci haka.


Karshe Zainab ta ce:"Bari na kira ummah ku gaisa",Ahmad ya ce toh Zainab ditah, bayan ta kira ummah.Ummah ta zo,taga surukinta,ta nuna kaunarta kan lamarin su gaisa.Karshe ta musu addu'a kan Allah ya bada sa'a,ta ce:"mun gode da ziyara",cikin kunya Nura ya ce Ilahi,Amin ummah mun gode muma,hahaha Ahmad kuwa shuru kake jinsa duk zaqin muryasa ya kare kan Zainab.Karshe bayan umma ta fita se Nura ya ce:"toh ya kamata mu koma saboda dare ya hanzarto".Zainab ta kalli Nura cikin wasa ta ce:"Uhmm.Wato bamu gama ganawa ba ne,zaka dauke min shalele nah".Toh shikennan muje na raka ku.Wata rana za tazo se da izini na ya fito ehem.Zainab takai su kofar gida,su yi sallama su tafi.Zainab da Ahmad kowa na kewar kowa.


Mu hadu a kashi na 5,in Allah ya hadamu don jin ya soyayyarsu zata dawo,daduwa zata yi ko raguwa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post