Rbtw: Jameel J.I.R
Ahmad yana bacci,cikin dare yayi irin farkawar nan,ya jawo handset don kunna haske,ya ci karo da wanan reply na muradinsa Zainab,wanda xuciyarsa ta dade da jira irin wanan sakon.Ya karanta yana mai zumudi da murna,domin kuwa ya samu abun da xuciyarsa take fata.A nan tunaninsa ya kau,farin-cikinsa ya zau,Ahmad ya daga kai sama tare da hannuwansa yana mai cewa:"Alhamdullah!,Allah mai amsa addu'an bayinsa,ka jinkirtamin, amma jinkirin ya zamo alkhairi gareni.Allah ka sanya tausayi,da kauna a tsakaninmu.Ka tabbatar mana da alkhairi a tsakaninmu,ka sanya soyayya ce mai riba a tarayyarmu.
Washe gare ya sami abokinsa Nura cikin annashuwa ya basa labari,yau Allah ya mallaka masa Zainab.Abokinsa Nura ya tayasa murna,ya kuma basa wasu shawarori don ganin Ahmad ya tafiyar da soyayyarsu ba tare da matsalaba.
Ahmad da nurul qalbinsa Zainab suka ci gaba da shan soyayyar su,ba tare da wata matsalaba.Har su koma WhatsApp,kowa ya turawa kowa pics nasa.Abun ya Kara girma, shakuwa ya karu,rayuwarsu tayi fari-sal.
Wata rana Zainab ta nema ganin Ahmad akan ya kawo mata ziyara don suga juna ido-ido,Ahmad ya aminta,ya saka ranan da zai je.Zainab ta yi murna sosai.
Ranar nan da Ahmad ya saka ta zo.Ahmad ya ci kwalliya,ya kira abokinsa Nura kan ya zo su tafi,Jim kadan se ga Nura ya zo.Suka dau hanya zuwa ga zinariyar Ahmad.
A lokacin ita kuma Zainab itama ta ci kwalliya,ta dafa abinci mai dadi,harda nama ciki.Zainab ta shirya komai tsaf,jiransu take kawai,ta kira Ahmad ya ce:"muna hanya yanzu haka muna gab da isowa.
Mu hadu a kashi na 4,in Allah ya hadamu don jin ya Ahmad da abokinsa zasu kasance a gidansu Zainab.