Rbtw:J. I. R.
Ahmad yana kwance a kan kujera,yana tunanin ta yanda zai fara,kawai ya ciro handset nasa,ya shiga wurin text message,bayan da ya shiga se ya fara text,yana mai introduction din Kansa kamar haka,yana cewa:"Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu,ni'imar Allah da yalwarsa su sauka gareki ya kammalalliyar mace.Nasan da zaki nemi sanin suna na,da suransu,wanda shi ne abu na farko da duk wani wanda bai sankaba yake bukata,in sha Allah ina mai ce miki hakan abu ne mai sauki gareni,in bayyana miki haqiqanin waye ni.A farko sunana Ahmad kuma ni mutum ne kamar ke,garin da kike nan nake.Ni a yanzu ban bukatar sanin ko ke wacece,domin labari ya riske ni,ya nuna min da ke din mutumiyar kirki ce,mai tarbiya.
Zainab zan so ki fuskantu da tunaninki dari-bisa dari don ganin kin fahimce ni,kan kalaman da zan amfani dasu don isar da sakona izuwa gareki.Ina fatan zaki fahimci wanan sakon na zuciyata zuwa ga zuciyarki.Ya Zainab
Ya wacce take mai kyan hali da suran da baida misali a gareni.Ganin ki na farko,ya sanya zuciyata,ta aminta dake.Ki aminta da ita ya ma'abociyar tausayi da kamala.Zainab sonki ya shiga cikin bargon dake cikin kashu-shuwan cikin jikinah,ya ratsa ya shiga cikin-cikin zucitah.Kin zamto jinin jikinah a yanzu,ban bukatar komai daga gareki face ki ce kin amince dani a matsayin masoyinki.Lallai Zainab in da so yake nan kauna yake,Zainab ki aminta dani na aminta dake,zan so ki sani Ina sonki da gaskiya.
Zainab zuciyata,ta dade da shiga tarkon ki Zainab,tunani ya dade da yawa a kanki,idanuwa sun dade da ganin yanayin mallakar kyakyawar fuskarki Zainab.Zan so ki mallakamin kanki,zan nuna miki gata,ina tabbatar miki da cewa karshenta aure in sha Allah.Zan su ki duba sakon zuciya ki fada ra'ayinki game da sakon da zuciyata ta isar cikin lokaci,don ganin kin ceto tah a irin wanan yanayin da sonki ya kamata kamo haqiqanin kamu.Ina yiwa kaina fatan alkhairi.Na barki lafiya,se naga reply na.My hope.
Haka dai Ahmad yayi ta tura sako zuwa ga Zainab,tana karantawa amma bata replay,karshe dai Zainab tun bata gamsuba har ta gamsu.Hakan yasa ta bayyana ra'ayinta tana mai cewa:"Ban taba tunanin zan fada kogin so a yanzuba,don ganin Ina cikin yanayin karatu,haqiqa Ahmad ka zam mai sa'a cikin mazaje,domin kuwa naqi aminta da soyayyar kowa a baya,amma gashi zuciyata ta aminta da naka.Ina mai sanar da kai na damqama amanar zuciyata, don ganin kai ne zaka iya bata kulawar da duk take bukata,ina rokon Allah da ya sanya alkahiri.Na'aminta da soyayyarka Ahmad,I love you.You are My nice dream.You are my sweetheart.I'am so happy,you beloved my heart.
Mu hadu a Kashi na 3,don jin ya Ahmad zai tsinci Kansa bayan da Zainab ta amsa soyayyarsa.