Rbtw:J. I. R.
An yi wasu masoya a wani lokaci,sun so junansu kamar lafiya ga dan adam,wanda har sun kai da wannan matakin, da ake kira da "Hanta da jini".
Ahmad,a farkon soyayyarsu da Zainab,ta kasance ne,ya ganta, ganin farko bayan ta dawo daga school(KASU),ta zo wucewa.Wanan lokacin suna tare da abokinsa mai suna:Nura.A garinsu kaduna.Unguwan marafa.
Ahmad ya ce:"Abokina kaga wancan yarinyar?,Kai amma yarinyar tayi,ta hadu,irin kalar yaran gwamnonin nan.Kai gsky dama-dama...Budan bakin abokin nan Nura se ya ce:"Ai!,baka santa ba Ahmad,ai yarinyar Mallam Rabi'u ce.Ahmad ya ce:"Haba dagaske kakeh?,aiko zaka rakani anjima.Nura ya amsa masa da cewa:"toh abokina".
Bayan haka,se Ahmad ya kira wani abokinsa a waya,wanda yake kusa da su Zainab don jin takaitaccen labari kan Zainab,saboda ya san ta wana hanya zai bi don mika soyayyarsa har ya kai da ta amsa soyayyarsa.Abokin nan ya basa labari yana cewa:"Yarinyar gsky ita ba yar kowa ba ce,kuma halinta mai kyau ne,domin har yau,ba zan iya cewa ga wani namiji da take hulda dashiba,saboda tana da kamun kai da tarbiya.Bawai ba wadanda suka nema soyayyarta ba ne,a'a akwai su da su miko tayinsu,amma taqi amsa saboda ita karatu ne agabanta.Bayan abokin nan ya gama basa labari,se Ahmad ya zauna yana ta tunanin ta yaya zai fuskanci wanan yarinyar,saboda cikin labarin an bashi cewa taki amsan kowa saboda karatu ne gabanta.Nan dai ya daga wayarsa,ya kira abokinsa Nura akan yazo yanzu-yanzu don ganin sun tautauna,sun yi shawara an sami mafita.Bayan da Nura ya zo,Ahmad ya basa labarin yanda wancan abokin nasa ya bashi.
Se Nura ya kalli abokinsa Ahmad yace:"ka kwantar da hankalinka akwai mafita komai zamu kaima in da muke so in sha Allah.Ahmad ya kalli Nura ya ce:"Hankalina ba zai taba kwanciyaba,har sai naga na mallaki Zainab a matsayin abokiyar rayuwata",Nura don Allah ka fadimin,ya za'ayi?,Nura can yayi shuru yana tunani,bayan haka ya ce:"Ahmad na samu mafita.Nan Ahmad cikin sauri da rawar kai cike da farin-ciki ya ce:"Nura Fadi inajinkah abokin kirki",Nura ya ce:"Yanzu mu yi kokari mu sami phone number tah,in mu samu se,a zauna a tsara kalamai.Da farko ka sanar da ita kai waye,ka kuma bayyana mata hadafinka,karshe ka nema amsa.Ahmad ya karbi wannan shawarar hannu biu,ya daga waya ya kira wancan abokin nasa,dan kusa da su Zainab,ya ce:"Ya za ayi a nemo Masa phone number na Zainab,ya amsa da toh zan yi kokari.Bayan maganarsu da dan wasu mintoci,se Ahmad yaji shigowar text,yana dubawa ya ga phone number Zainab a turo masa.
Mu hadu a kashi na 2 in Allah ya hadamu,don jin Ahmad zai kira Zainab ne?,ko shawarar abokinsa zai dauka,ko kuma tsoro zai hana sa aikata ko daya.
Tags:
Taskar Ma'aurata