Kiran Mabiya Mazhabar Shi'a: A Yiwa Masu Zanga-zangar End SARS Adalci.


 

Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato


Wannan kiran ya fito ne daga bakin wakilin yan'uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky na yankin Sakkwato Sheikh Sidi Munir, ya kuma yi wannan kiran ne a Yau Lahadi 25/10/2020 a daidai lokacin da yake fira da manema labarai dangane da abubuwan da suke faruwa a kasarnan. Tun a farko Malamin ya soma ne da taya al'ummar kasarnan jaje kan abubuwan da suka faru a kwanakinnan wanda har takai ga salwantar rayuka da dimbin dukiyoyi.


Malamin ya cigaba da cewa, “Yin adalci ga mutum daya adalci ne ga kowa, saboda haka a yi adalci ga masu zanga-zangar END SARS da aka kashe, domin ba ta yadda za a yi ace ana zubar da jinin mutane a kasa bisa ga zalinci kuma a sami cigaba, dukkanin wadannan abubuwan da suke ta faruwa a kasa na dagulewar al'amurra baki daya ba zai rasa nasaba da alhukkan yan kasa da na jinanen da ake ta zubarwa na wadanda basu ji ba basu gani ba”.


Ya kara da cewa, “tun farkon mulkin Buhari ya fara shi ne da zubar da jini, inda a shekararsa ta farko ya tura rundunar Sojoji suka budewa yan Shi'a almajiran Sayyid Zakzaky wuta a Zariya da sunan tare hanya, inda suka kashe sama da mutum dubu daya.


Matsalar End SARS matsala ce ta cin zarafin da jami'an hukumar SARS ke yiwa yan Kudu ba kamar yadda wasu ke kokarin juya matsalar da sunan rikicin addini ko kabilanci ba, matsala ce wacce muma muke fama da ita anan, ta inda ya zamana a kodayaushe rundunar yan Sandan jahar Sakkwato karkashin jagorancin Kwamishina Ibrahim Sani Ka'oje ke cin zarafinmu da tauye mana hakkinmu na addini, wanda ko a bara yan Sandan sun bude mana wuta har suka kashe mana yan'uwa biyu”.


A karshe kuma ya kara da yin kira ga mahukuntan kasarnan da su yi adalci ga Sayyid Zakzaky da suke cigaba da tsarewa fiye da shekaru biyar Yau, wanda kuma suka kashewa 'ya'ya shida tareda almajiransa sama da dubu daya, su kuma sakeshi kamar yadda kotu ta yi umurni tare da biyan shi diyya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post