@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KYAWAWAN 'DABI'U KAYAN ADO GA MUTUM
Fulani qabila ce wacce suke da tsananin riqo ga al'ada, sannan kuma masu tsananin aqida wacce ko addini ne bai cika iya raba su da ita ba.
Duk wanda yasan Fulani kuma yake mu'amala dasu zai iya gaskatani cewa suna da wata aqida ta qyamatar hada auratayya tsakaninsu da wata qabila, musamman ma Fulani mazauna karkara.
Yawancinsu sunfi so su hada aure a zumunce don qara qarfafa zumuncinsu, Idan kaga Bafulatani ya auri Bafulatana to, ka bibiya a hankali za ka tarar suna da dangantaka ta jini. Idan kuwa kaga anyi aure ba cikin dangi ba, to, in kayi bincike za kaga suna da dangantaka ta qabila.
Wannan aqida tasu ta yi tasiri sosai cikin zukatansu har ga 'yan'uwa 'yan gwagwarmaya.
Akwai wani dan'uwa mai qoqari wajen bada gudumawarsa a harka ta bangaren jiki, lokaci da kuma dukiya. Amma wani lokaci muna hira cikin 'yan'uwa game da yanayin dabi'un 'yan'uwa ana tattauna cewa ba kawai don mutum ya amsa sunan dan harka ne za ka dau 'yarka ka bashi ba, a'a, dole ya kasance mai kyawawan dabi'u wadanda ke tafiya daidai da koyarwar harka islamiyyah.
Ana cikin haka sai wannan dan'uwa Bafulatani ya bude bakinsa yace;
" KUN GANNI NAN ! WALLAHI HAR GOBE INA DA AQIDAR KO DA ACE MUTUM 'DAN'UWA NE IN HAR BA BAFULATANI BANE BA ZAN BASHI 'YATA BA. AMMA KAGA MALAM (yana nufin ni) SABODA 'DABI'UNSA DANA YABA, DA ACE ZAIGA WATA 'YA CIKIN 'YA'YANA YACE YANA SO, WALLAHI ZAN BA SHI !"
Wannan yabo nasa gare ni ya girgizani sosai, ace wai kyawawan dabi'u na ne za su iya canza aqidarsa har yaso abinda baya tunanin zai iya sonsa.
Na gode Allah da jin wannan furuci nasa, domin hakan ya qara min qwarin gwiwa wajen cigaba da aikata abinda nake yi. Da ace munanan dabi'u nake yi wadanda zai qyamace ni kuma har na gane, to, da ya taimake ni domin zan gyara.
Allah (T) na cewa;
" KUMA GAME DA NI'IMAR UBANGIJINKA (da yayi gare ka) KA BADA LABARI ."
Yin hakan na daga cikin godiya gare shi. Kuma ya qara da cewa;
" IDAN KUKA GODE (kan ni'imar da yayi muku ta farko) ZAN QARA MUKU ."
To, ina nuna godiyata gare ka yaa Allah bisa wannan ni'ima da kayi min, kuma ina neman qarin wata gare ni, domin kai ba ka saba alqawari.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
19th October, 2020/ 2nd Rabi'ul-Awwal, 1442.