Kamanceceniyar Mulkin Buhari Dana Fir'auna !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KAFUWAR ADDINI SUKE JIN TSORO KUMA ZAI TABBATA 

A tarihin duniyar magabata ba a taba samu ko yin shugaba azzalumi wanda ya daukaka a doron qasa kamar Fir'auna ba. 

Ya samu a tarihi da kuma wajen Bokayensa cewa akwai wani yaro da za a haifa a zamaninsa wanda zaiyi sanadin gushewarsa daga mulki da kuma kafa wani addini wanda shine zai mamaye duniya, sannan zai daukaka wadanda ake gani sune maqasqanta. 

Wannan dalili yasa Fir'auna ya qara daukaka kansa a matsayin shine Ubangiji mafi daukaka, kuma ya sanya jama'arta qungiya-qungiya, ya riqa azabtar da wadanda ba ya so yana barin wadanda yake so .

Shi kuma Allah mai iko akan komai da kowa ya bar shi cikin wannan zalunci zuwa wani lokaci , a qarshe ya qasqantar da shi kuma ya daukaka bayinsa muminai. 

Ku biyo mu cikin wadannan ayoyi don gaskata maganarmu. 

إِنَّ فِرۡعَوۡنَ عَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَجَعَلَ أَهۡلَهَا شِيَعٗا يَسۡتَضۡعِفُ طَآئِفَةٗ مِّنۡهُمۡ يُذَبِّحُ أَبۡنَآءَهُمۡ وَيَسۡتَحۡيِۦ نِسَآءَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ ٤ 

" LALLE FIR'AUNA YA 'DAUKAKA (kansa) CIKIN QASA, SAI YA SANYA JAMA'ARTA QUNGIYA-QUNGIYA YANA RAUNATA WATA JAMA'AH DAGA GARE TA, YANA YANYANKA 'YA'YAYENSU (mazaje) YANA RAYAR DA 'YA'YAYENSU (mata). LALLE SHI YA KASANCE DAGA CIKIN MASU BARNA !"

Za muga irin abinda Buhari yake yi kenan a yanzu ko ma yana yin fiye da haka. Domin ya raba jama'ar qasar yana rayar da wasu daga cikinsu kuma yana karkashe wasu daga cikinsu.

Fifikonsa akan Fir'auna shine, Fir'auna ya taqaita kisansa ne kawai akan 'ya'ya (maza) yana barin mata, sannan tarihi bai kawo cewa Fir'auna yana qona gawarwakin wadanda ya kashe ba. Shi kuwa Buhari bai ware tsakanin mata da maza ba, dukkansu kashewa yake yi har ma da qona gawarwakinsu, waqi'ar Zaria babban misali ne. 

Shi kuwa Allah (T) nufinsa shine ya daukaka wadannan raunana cikin ikonsa. Saboda haka ya bayyanar mana haka cikin ayar da ke biye

وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱسۡتُضۡعِفُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنَجۡعَلَهُمۡ أَئِمَّةٗ وَنَجۡعَلَهُمُ ٱلۡوَٰرِثِينَ ٥

" KUMA MUNA NUFIN MUYI BAIWA (ne) AKAN WADANDA AKE RAUNATAWA CIKIN QASA (ta hanyar karkashe su da naqasarwar da ake musu ), KUMA MU SANYA SU JAGORORI (a makwafin wadannan azzalumai) KUMA MU SANYA SU MAGADA ."

Ya qara da cewa; 

وَنُمَكِّنَ لَهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَنُرِيَ فِرۡعَوۡنَ وَهَٰمَٰنَ وَجُنُودَهُمَا مِنۡهُم مَّا كَانُواْ يَحۡذَرُونَ ٦

"KUMA MU ZAUNAR DASU CIKIN QASA (suna juyata bisa tsarinMu) , KUMA MU NUNAWA FIR'AUNA DA HAMANA DA RUNDUNARSU (tabbatuwar )ABINDA SUKE JIN TSORONSA (na tabbatuwar addini) !"

(QASAS, AYA TA 4-6)

Alqawarin Allah kuwa ya tabbata, domin ya tabbatar da abinda Fir'auna ke tsoron tabbatuwarsa, kuma ya daukaka wadanda aka raunata suka zama sune madaukaka masu juya qasar bisa umarnin Ubangijinsu. 

Kowa ya sani ba wani abu Buhari ke jin tsoro ba sai tabbatuwar addinin Allah, domin tabbatuwarsa yana qasqantar da azzalumai wadanda suka daukaka kansu, sannan yana daukaka raunana muminai da aka qasqantar da su, su zama sune madaukaka masu fada a ji. 

Babu kokwanto cikin wannan magana ga masu hankali da tsoron Allah kan cewa tabbatuwar addini Buhari ke tsoro, domin za muga yana tafiya sau-da-qafa tare da masu nuna cewa mulkinsa na Allah ne, wato 'yan Izala da kuma Yahudawan dake goya masa baya wajen dishe hasken Allah. 

Su kuwa masu qoqarin tabbatar da tsarin Allah suka zama sune raunana abin raunatarsa cikin qasa.  

" LALLE ALQAWARIN ALLAH GASKIYA NE, KADA WADANDA BA SU DA YAQINI SU BAKA TSORO ."

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 

✍🏼Tare da Ado Isah Guda. 

       (08126385470)

    22nd October, 2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post