@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KAI MALAMINKA CIKIN WANNE AJI KAKE ?
Imam Sadiq (A. S) yayi mana bayanin yadda mutane suka karkasu gwargwadon yadda suke, kuma yayi mana nuni ga abinda ya kamata muyi gare su.
Ku biyo ni cikin wannan hadisi da ke biye
رُوِيَ عَنْ بَعْضِ الصَّادِقِينَ ع
" أَنَّ النَّاسَ أَرْبَعَةٌ رَجُلٌ يَعْلَمُ وَ يَعْلَمُ أَنَّهُ يَعْلَمُ فَذَاكَ مُرْشِدٌ عَالِمٌ فَاتَّبِعُوهُ وَ رَجُلٌ يَعْلَمُ وَ لَا يَعْلَمُ أَنَّهُ يَعْلَمُ فَذَاكَ غَافِلٌ فَأَيْقِظُوهُ وَ رَجُلٌ لَا يَعْلَمُ وَ يَعْلَمُ أَنَّهُ لَا يَعْلَمُ فَذَاكَ جَاهِلٌ فَعَلِّمُوهُ وَ رَجُلٌ لَا يَعْلَمُ وَ يَعْلَمُ أَنَّهُ يَعْلَمُ فَذَاكَ ضَالٌّ فَأَرْشِدُوهُ."
FASSARA
-------------------
" LALLE (su) MUTANE (kashi) HUDU (4) NE.
(1)- MUTUM WANDA YA SANI (mai ilimi) KUMA YA SAN CEWA YA SANI, WANNAN SHINE MALAMI MAI SHIRYARWA, KU BI SHI (don ku ma ku sami shiriyar ) .
(2)- DA MUTUMIN DA YA SANI AMMA (shi) BAI MA SAN YA SANI BA, TO, WANNAN GAFALALLE KU FARKAR DA SHI (in ba haka ba ba zai iya yin abinda zai amfanar da shi ba ballantana yayi abinda zai amfanar da wasunsa .
(3)- DA MUTUMIN DA BAI SANI BA, KUMA BAI MA SAN BAI SANIN BA, TO, WANNAN JAHILI NE KU SANAR DA SHI (don shima ya rabauta .
(4)- DA MUTUMIN DA BAI SANI BA, KUMA (shi) A TSAMMANINSA YA SANI NE, TO, WANNAN BATACCE NE KU SHIRYAR DA SHI (don in ba kuyi hakan ba ba zai taba bin wanda ya sani ba balle ya rabauta ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 196
Duk mai hankali wanda ya nutsu zai iya gane kowanne irin mutum a wanne aji yake, kuma zai san wanne irin wannan mutumi ke buqata.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08137925034
30th Sep, 2020/ 13th Safar, 1442.
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com