A jawabinsa na farko bayan zama zababben shugaban kasan Nijeriya, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin gudanar da nagartacciyar gwamnati da kiyaye dokokin kasa. Akalla da ya iya cika wannan alkawari, da wannan ma ya isa. Wannan dalilin ne ya sa kaina ya daure lokacin da labari ya riske ni cewa sojoji sun mamaye gidanmu a Zariya domin yin kisan kiyashi. Na tsimu, yayin da kunnuwana suka fara jiyo rugugin fashewar gurneti, saboda sam! Ban taba sawwala cewa zai yiwu a kaddamar da irin wannan ta’asa a kan dan adam ba.
Sojojin Nijeriya ne suka farmaki Mahaifiyata da Mahaifina a gidanmu. Da karfin tsiya sojojin suka yi ta kisa tare da kona mutane har suka kai ga gidanmu. Haka suka kashe duk wadanda suka taras a gidan, tare da tarwatsa komi. Wani karin abin mamakin shi ne yadda Buhari da gwamnatinsa suka kyekyashe kasa wurin yin amfani da duk wata dama wurin yin kwaskwarima ga wannan kisan gilla da suka aikata.
Bayyanannen abu ne cewa, an kulle iyayena na tsawon shekaru ba bisa ka’ida ba.
Bayan da suka tabbatar da sun kure wa ramin karya, sai suka fara yada cewa suna kasha Naira miliyan biyar duk wata wurin boye mahaifana da suke yi. Alhali dukkanin wasu matakan shari’a da aka bi, an yi nasarar samun hukuncin cewa a sake su, ba su da laifi. Sai dai kash! Gwamnati ce da ba ta mutunta umurnin kotu. Sun dai kware wurin yada farfaganda da karya.
Tunda suka samu nasarar yi wa Mahaifina da Mahaifiyata bakin fenti da cewa su ‘yan Shi’a ne, sai suka rika yin amfani da wannan wurin halasta kisan kiyashin da suka aikata. Tun daga sannan, duk wani da aka lakabawa sunan shi’a, sai a ci mutuncinsa, a zalunce shi, a kashe shi ko a kashe su komi yawansu, sannan a yi musu kabarin bai-daya ba tare da jami’an tsaron (FSARS ko sojoji) sun bayar da daman yi musu jana’iza ba.
Gwamnati ta nuna ba ta shirya tsagaita wannan tsari na ta na tallata rashin tsaro da cin zarafi, farfaganda da kisa a matsayin hanya guda daya ta cimma muradin gwamnatin Buhari da dandazon mabiyansa. Da jimawa wannan shi ne abin da ke faruwa a Arewacin Nijeriya; ta yadda ba ma zai yiwu ka iya yin tukin kilomita 70 daga Zariya zuwa Kaduna ba tare da fargabar ‘yan bindiga za su iya sace ka ko a kashe ka a hanya ba. Su wadannan ‘yan bindigan suna bayyana ne kawai, su sace mutane, su kwace dukiya, su yi kisa sannan su sake bacewa.
Salon tarwatsawa da rusawa na ci gaba da samun wurin zam a arewacin Nijeriya, inda ta ke shafar kusan kowa, har da wadanda ke shiru tare da goyon bayan irin abubuwan da gwamnatin Buhari ke aikatawa.
A karshe dai, irin wannan salon na kyamata, azabtarwa, cin mutunci da kisa sun haifar da yanayin da wasu sun nuna sun gaji, har ta kai ga sun nuna damuwarsu.
Taken nasu shi ne a kawo karshen rundunar SARS, rundunar da an yi imanin cewa sun fi kowanne rashin Imani a gwamnatin Buhari. Da farko gwamnatin Buhari ta nuna ta aminta da bukatun masu zanga-zanga, har ta sauyawa SARS din zuwa SWAT. Wanda wannan bai isa ya zama dalilin tsagaita zanga-zangar ba.
Daga nan sai gwamnatin ta dauki matakin amfani da karfi domin dakile wannan yunkuri.
Salon nasu dai bai canza ba, shi ne yin daukar nauyin matasan da ke zaman banza wurin sata da kone-kone. Irin wadannan matasa marasa Imani su ne suka yi ta yanke dan yatsan gawa domin su sace zobe, kamar yadda ya faru a Zariya a watan Disambar 2015. Ba ta gajiya da irin ta’asar da ta kwashe shekara biyar 5 tana aikatawa a arewa na kisa, fyade da sauransu yanzu irinsa suke son yi a sauran sassan Nijeriya. Suna biyan wasu ‘yan miskinan kudade ga wadannan matasa domin su tare hanya, su kashe rayuka, su tarwatsa mutane.
Sun dade suna aikata irin wannan barnar a Jihohin Kaduna, Katsina, Kebbi, Zamfara, Borno, Yobe da sauran sassan arewacin Nijeriya.
Domin su samar da wani yanayi da zai farfado da kimar Buhari, suna ta kokarin kunno wutar rikicin kabilanci, rikicin bangaranci da rikicin addini, ta yadda za a yi barna da sunan bangarancin kudu da arewa.
Duk fa da irin haka ne gwamnatin ta Buhari ke son halasta irin kisan mummuken da shugaban makasansa Buratai ke jagoranta. Wadannan mutanen da sunansu ya fara da Kalmar ‘B’ ne alhakin rashin zaman lafiyan da ke faruwa a Arewacin Nijeriya ya rataya a wuyansu, kuma burinsu shi ne su kai wannan rashin lafiya zuwa wasu sassa, har ma wasu kasashen idan da hali. A yanzu haka, ‘yan bindigan da suke aiki da su, suna ta kokarin rura wutar rikicin bangaranci a fadin Nijeriya, ta yadda za su ci gaba da aiwatar da kisan kai.
Mahaifina Ibrahim Zakzaky asalinsa Hausa Fulani ne, wannan bai tseratar da shi daga muguntar B+B ta Buhari da Buratai. Mahaifiyata Bayarbiya ce, wacce Mahaifinta ya fito daga Ibadan, mahaifiyarta daga Ilorin, amma wannan bai sa an iya barinta ta samu tiyata a gwiwarta ba, don kawai B+B ne suke mulki a Nijeriya.
Tuni wadannan tawaga ta B+B ta ragargaji wani bangare na Nijeriya. Yanzu dai tabbatar muggan makaman da aka nema aka rasa a Sambisa ashe suna hannunsu, domin da su ne suke tabbatar da an ci gaba da sace mutane ana kashe wanda ake so. Sai dai idan kuma an ki biyewa tsarin B+B na a raba-don a mulka.
Jini da tsoka ina tare da duk wani motsi da aka assasa shi domin neman adlci a Nijeriya, ko da kuwa menene sunan wannan motsin. Damuwata daya ita ce, sai zuwa yaushe ne za a farga daga irin zalunci da kisan da gwamnatin Buhari bisa ja-gaban Buratai ke aiwatarwa a fili da boye?
_Mohammed ya rubuto ne daga garin Zariya da ke Jihar Kaduna_
Saƙo ya isa,madalla.
ReplyDelete