@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABU MARABARSA DA MAI YIN GUDU A DOKAR DAJI DA SUNAN YANA NEMAN HANYA
Ya zo cikin riwaya daga Imam Sadiq (A. S) yana cewa,.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
الْعَامِلُ عَلَى غَيْرِ بَصِيرَةٍ كَالسَّائِرِ عَلَى غَيْرِ الطَّرِيقِ وَ لَا يَزِيدُهُ سُرْعَةُ السَّيْرِ مِنَ الطَّرِيقِ إِلَّا بُعْداً.
" SHI MAI YIN AIKI BA BISA ILIMI BA KAMAR MAI SAURI NE A GURIN DA BABU HANYA, WANNAN SAURIN TAFIYA NASA BA ZAI QARA MASA KOMAI BA DAGA (fadawa kan) HANYA SAI DAI DADA NISANTAKA ."
لي، الأمالي للصدوق الْعَطَّارُ عَنْ أَبِيهِ عَنِ ابْنِ عِيسَى عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنِ ابْنِ مُسْكَانَ عَنِ الْحَسَنِ بْنِ زِيَادٍ الصَّيْقَلِ قَالَ سَمِعْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ الصَّادِقَ ع يَقُولُ لَا يَقْبَلُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ عَمَلًا إِلَّا بِمَعْرِفَةٍ وَ لَا مَعْرِفَةَ إِلَّا بِعَمَلٍ فَمَنْ عَرَفَ دَلَّتْهُ الْمَعْرِفَةُ عَلَى الْعَمَلِ وَ مَنْ لَمْ يَعْمَلْ فَلَا مَعْرِفَةَ لَهُ إِنَّ الْإِيمَانَ بَعْضُهُ مِنْ بَعْضٍ
Wannan riwaya kuma da aka samo daga Hassan Bn Ziyad As-Saiqali yace, na ji Abu Abdullah ( Imam Ja'afar (A. S) yana cewa,
" ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA BA YA KARBAR AIKI HAR SAI DA ILIMI (na sanin hukuncin wannan aiki), HAKAMA ILIMIN (ba ya amfani) HAR SAI (an hada shi) DA AIKI. DUK WANDA YA SANI (to wannan sanin nasa) ZAI YI MASA NUNI ZUWA GA AIKI , WANDA KUWA BAI YI AIKI (da abinda ya sani ) BA, TO, BA SHI DA ILIMI. LALLE (shi) IMANI SASHENSA
DAGA SASHE YAKE (abu guda ne kamar dai yadda yake ba a raba ilimi da aiki ."
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 207
Wannan hadisi na farko yazo daidai da fadin Allah (T) cikin wani hadisil-Qudsiy inda yake cewa ,
" KU SANNI KAFIN KU BAUTA MIN, IDAN BAKU SANNI BA TA YAYA ZA KU BAUTA MIN ?"
Dole ya zamana in za ka tafi gari ya kasance ka san hanyar zuwa ko da kuwa ta hanyar tambaya ne. Duk wanda bai san gari ba kuma bai tambayi wanda ya san shi ba, to, ba zai iya zuwa garin ba. Kuma ko da ya shiga cikinsa ba zai san shi bane dole sai yayi tambaya.
Shi kuwa hadisi na biyu na nuna mana ne cewa duk wani aikin da mutum zai yi matuqar babu ilimi cikinsa Allah ba zai karba masa ba. Sannan kuma ba a gane ilimi sai ta hanyar aiki.
Duk wanda yasan wani abu amma ba ya aiki da shi, to, sunan wannan sanin nasa karatu ba ilimi ba, domin ilimi shine wanda ake aiki da shi.
Wai, ashe yanzu masu karatu muke da su ba masu ilimi ba, shi yasa suke da'awar aikata fasadi ba ta kawo gyara ba.
" SUNE WADANDA SUKE YIN BARNA CIKIN QASA BA SA YIN GYARA !"
Allah ka bamu Ikon neman ilimi da kuma yin aiki da shi .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
(08126385470-08137925034).
25th October, 2020/ 9th Rabi'ul-Awwal, 1442.