🌿🌿🌿🌿🌿🌿
Abbagano✍️
Na zaɓi nayi wannan rubutun ne domin haskawa ƴan uwana ɗalibai wasu abubuwa don su fahimci al'amarin mauludi bawai sabon abune wanda ba'ayi shiba a can baya.
Rubutu na, zanyi shi dakiki ne,
√ Na farko: hujjar maulud cikin Alkur'ani
√ Na biyu: hujjar maulud cikin sunna, wato hadisai.
√ Na uku: hujjar hankali akan yin mauludi.
√ Na huɗu warware shubuha akan maulud.
√ Na biyar illolin rashin yin maulud ga al'ummar annabi
ALKUR'ANI MAI GIRMA
1- hujja ta farko dazan fara aiki da ita, itace hujjar alƙur'ani mai girma, domin shine farkon tushen da ake komawa gareshi don kafa hujja
قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ
يونس (58) Yunus
Ka ce: "Da falalar Allah da rahamarSa. Abisa haka Sai su yi farin ciki da wannan." Shĩ ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa.
Acikin wannan ayar zamuga umarnin da Allah (t) yayi mana, nayin farin ciki akan wata rahama,
Idan mukai duba da kyau, zamu tabbatar babu wata rahama da takai samuwar annabi Muhammad (s) domin Allah ma dakan sa yagayawa Manzon sa!!!
وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا رَحْمَةً لِّلْعَالَمِينَ
الأنبياء (107) Al-Anbiyaa
Kuma ba Mu aike ka ba fãce dõmin wata rahama ga talikai.
________________
Idan mukai lura, sosai da sosai zamuga cewar wannan ayar ta Alkur'ani ta nuna mana yin farin ciki lokacin da wata rahama ta same daga Ubangijin ka,
Sannan aya ta biyu ta nuna mana, babu wata rahama da takai aiko, annabi.
To bisa wannan ne muke nuna farin cikin mu da samuwar wanda aikoshi garemu yazama rahama,
Mu haɗu rubutu nagaba don jin hujja daga littafan magabata