@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
BABU NASSI DAKE NUNI KAN KHALIFANCINSA
Cece-kucen da aka samu bayan wafatin Annabi (S. A. W. W) shine waye zai zama Khalifa wanda zai jagoranci al'ummarsa a bayansa .
Akwai wadanda ke cewa Annabi (S. A. W. W) yayi wasicci ne game da Imam Ali (A. S) cewa shi zai jagoranci al'umma a bayansa wanda zai tafiyar dasu daidai kan abinda ya barsu a kansa. Sai dai kuma ba hakanne ta faru ba a zahirance, domin wannan wasicci bai yiwa mafi yawan Sahabbai dadi ba.
Wannan dalili yasa Annabi (S. A. W. W) na yin wafati kafin ma a bisne shi akayi wani taron sirri a Saqeefah don canza wannan wasicci na Annabi (S. A. W. W).
Ka san duk abinda aka sako son zuciya cikinsa sai anci karo da matsaloli. Saboda haka aka sami sabani kan waye zai maye wannan matsayi.
Rashin samun daidaito a tsakaninsu sai kawukansu suka rabu gida biyu, mutanen Makkah suka ce daga cikinsu za a fitar, yayin da mutanen Madinah ke cewa daga cikinsu za a fitar. Da aka kasa samun mafita sai kowa yace su fitar da Khalifah daga cikinsu.
Wani abin mamaki shine, daga mutanen Makkah masu son fitar da Khalifah daga cikinsu don su sabawa umarnin Annabi (S. A. W. W) sun rasa wata qwaqqwarar hujja abin dogaro. Saboda haka sai suka shiga kame-kame.
Ku biyo mu cikin wannan riwaya don jin hujjar da Umar ya dogaro da ita har yayi rinjaye.
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
- حَدَّثَنَا مُعَاوِيَةُ بْنُ عَمْرٍو ، حَدَّثَنَا زَائِدَةُ ، حَدَّثَنَا عَاصِمٌ . وَحُسَيْنُ بْنُ عَلِيٍّ ، عَنْ زَائِدَةَ ، عَنْ عَاصِمٍ ، عَنْ زِرٍّ ، عَنْ عَبْدِ اللَّهِ ، قَالَ : لَمَّا قُبِضَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ ، قَالَتْ الْأَنْصَارُ : مِنَّا أَمِيرٌ وَمِنْكُمْ أَمِيرٌ ، فَأَتَاهُمْ عُمَرُ ، فَقَالَ : " يَا مَعْشَرَ الْأَنْصَارِ ، أَلَسْتُمْ تَعْلَمُونَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَدْ أَمَرَ أَبَا بَكْرٍ أَنْ يَؤُمَّ النَّاسَ ؟ فَأَيُّكُمْ تَطِيبُ نَفْسُهُ أَنْ يَتَقَدَّمَ أَبَا بَكْرٍ ؟ فَقَالَتْ الْأَنْصَارُ : نَعُوذُ بِاللَّهِ أَنْ نَتَقَدَّمَ أَبَا بَكْرٍ " .
Mu'awiyata Bn Amriy ya bamu labari, Za'idatu ya bamu labari, Aseem da Hussaini Bn Aliyu sun bamu labari, daga Za'idatu daga Aseem, daga Zeer, daga Abdullahi yace;
Yayin da Annabi (S.A.W.W) yayi wafati sai mutanen Madinah suka ce;
" MU FITAR DA SHUGABA DAGA CIKINMU KU MA KU FITAR DA SHUGABA DAGA CIKINKU ."
Sai Umar yaje musu yace;
" YAA KU MUTANEN MADINAH, ASHE BAKU SAN CEWA ANNABI YA UMARCI ABUBAKAR DA YA JAGORANCI MUTANE (a sallah) BANE ?"
YANZU CIKINKU WAYE ZUCIYARSA TAYI MASA DADI YA GABACI ABUBAKAR? "
Sai Ansar suka ce ;
" MUNA NEMAN TSARIN ALLAH DA MU GABACI ABUBAKAR ."
(Musnad Ahmad)
Kunga ashe ba nassi bane yayi nuni da cewa Abubakar Khalifa a bayan Annabi (S. A.W.W) ba, sai dai ba'ayin Umar wanda wasu suka goya masa baya ido a rufe ko kuma shaqawa tayi musu yawa sakamakon bin son zuciyarsu.
Allah ka raba mu da bata bayan shiriya.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08126385470)
12th October, 2020/ 25th Safar, 1442.