@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DAGA ZANTUKAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S)
A duk lokacin da Imam Ali (A. S) yayi magana sai ka ga hikima a bayyane, duk da cewa wasu ba sa fahinta sai kayi musu bayani.
Zantukansa (A. S) sun sha bamban dana wasu, domin Idan ka ji wata magana daga wani sai kaga babu hikima ciki ko kadan.
Misali, " WANDA YAKE BAUTAWA ALLAH TO, ALLAH NA RAYE. AMMA WANDA YAKE BAUTAWA MUHAMMADU TO, MUHAMMADU YA MUTU ."
A tunanina dai kaf tarihi ba a taba samun wasu wadanda suka furta cewa Muhammad (S. A. W.) suke bautawa ba ballantana a qalubalance su.
Imam Ali (A. S) na cewa;
" ينبئ عن عقل كل امرئٍ لسانه ."
" HARSHEN MUTUM KE BADA LABARI AKAN HANKALIN KOWANNE MUTUM ."
Wallahi hakane, domin sau da yawa in kana mu'amala da mutane ba za ka fahinci haqiqanin su suwaye ba har sai mutum yayi magana za ka iya fahintar shi wanene.
Anan ne za ka iya fahintar shi wawa ne,
Mahaukaci ne,
Mai ilimi ne,
Dolo ne ko kuma
Gabo ne.
J U M U AT
U
B
A
RAK !
DAGA A
D
O ISAH GUDA.