Harkar Karatu A Nigeria, Gwamnati Ta Gaza !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A daidai lokacin da ministan ilimi ya sanar da lokacin bude makarantu ranar 12-10-2020 don cigaba da karantar da yara wadanda suka fada cikin matsalar karatu sakamakon sabuwar siyasar da hukuma ta qirqiro don cutar da al'ummarta da 'ya'yanta ta fuskacin karatunsu, yanzu su fito da wani sabon salo. 

Dokar da aka fitar ko sharadin da aka gindaya kafin dalibai su koma makaranta don cigaban karatunsu shine, dole ya kasance anyi feshi (spray) cikin kowanne aji. 

Sannan kuma dole ne hukumar makaranta ta biya adadin kudi dubu biyar (#5,000) a kowacce makarantar da ke da ajujuwa (classes) da basu kai goma ba. 

Idan kuma ajujuwa (classes) sun kai goma zuwa sama, to, dole su biya dubu goma (#10,000) kafin ayi musu wannan feshi (spray). Gwargwadon yawan ajujuwanku gwargwadon kudin da za ku biya. 

Saboda haka akace kowanne dalibi zai biya dari biyu (#200) kafin a karbe shi a makaranta. Sai dai kuma ganin ance dole sai anyi wannan feshi kafin a bude makaranta yasa malamai da hukumar makaranta (S. B. M. C) suke biyan wadannan kudade. Idan dalibai suka dawo kuma zai a karbi wadannan kudade daga hannunsu don a mayar abinda aka kashe, da kuma sayen abin wanke hannu (sanitizer). 

Sannan kuma doka ce ga kowanne yaro ya shiga aji da takunkumi (mask) kafin a barshi. 

Yanzu dai abinda iyayen yara ke fada shine, makarantu gwamnati sun dawo na kudi (privates). 

Gaskiya abin kunya ne ga gwamnati ace ta kasa sayen maganin da za ayi feshi cikin makarantu da kuma saya musu (mask), alhali sun sami maqudan kudade da sunan yaqi da cutar Corona (Covid-19).

Tare da Ado Isah Guda 

5th October, 2020/ 18th Safar, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post