@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA SHI AKE HUKUNTA MUTUM WAJEN HISABI
Hankali ya zama babban ma'auni wanda ake amfani da shi wajen auna abubuwa da dama don asan matsayinsu. Da shi ake bambance tsakanin dabba da mutum, kuma da shi ake cire dabbobi daga cikin mutane, sannan da shi ake hukunta mutum a duniya da kuma ranar hisabi.
Idan ka sami mutum wanda ba shi da hankali na halitta ba za ka hukunta shi ba, sannan kuma shi marar hankali a dabi'a ba ya rabauta.
Bambancin hankali a halitta da dabi'a shine, shi na halitta shine wanda Allah ya jarrabci bawansa da shi na tabuwar hankali (naqasu), to, shi wannan babu uquba a kansa.
Amma hankali na dabi'a shine wanda a zahirance mutum zai iya cewa ya fika a hankali da ilimi da kuma tunani, amma a aikace sai ta bayyana cewa ba shi da hankali don ba ya yin abinda zai amfanar da shi a duniya da lahira.
An samo riwaya wacce ta tuqe kan Abu Ja'afar da Abu Abdullah (A. S) suka ce;
- سن، المحاسن السِّنْدِيُّ بْنُ مُحَمَّدٍ عَنِ الْعَلَاءِ عَنْ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ وَ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالا
" Yayin da Allah ya halicci hankali sai yace masa ya juya (da baya), sai ya juya, sa'annan yace masa fuskanto (ta gaba) sai ya fuskanto, Sannan yace (T);
" NA RANTSE DA IZZATA DA 'DAUKAKATA, BAN HALICCI WATA HALITTA KAMARKA BA . ZUWA GARE KA NAKE YIN UMARNI KUMA ZUWA GARE KA NAKE YIN HANI. SANNAN KUMA ZUWA GARE KA NAKE BADA SAKAMAKO KUMA NAKE YIN UQUBA ."
لَمَّا خَلَقَ اللَّهُ الْعَقْلَ قَالَ لَهُ أَدْبِرْ فَأَدْبَرَ ثُمَّ قَالَ لَهُ أَقْبِلْ فَأَقْبَلَ فَقَالَ وَ عِزَّتِي وَ جَلَالِي مَا خَلَقْتُ خَلْقاً أَحْسَنَ مِنْكَ إِيَّاكَ آمُرُ وَ إِيَّاكَ أَنْهَى وَ إِيَّاكَ أُثِيبُ وَ إِيَّاكَ أُعَاقِبُ.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج1، ص: 97
Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, umarni da hani ba ya hawa kan kowa sai ga mai hankali kadai, sannan ba a yin hisabi ga marar hankali (na halitta) wajen ba shi lada ko azabtar da shi sakamakon wani aiki da yayi ko ya qi yi wanda Allah yayi umarni ko hani a kansu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
3rd October, 2020/ 16th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com