Gare Ku Sisters: Me Ya Saka Alqaluman Sistocin Mu Ya Takaita Kan Warware Matsalolin Su Kawai??



 

Daga Bin Haroun Sigau

Assalamu Alaikum

Yan Uwa na mata wannan sako ne zuwa gare ku, yaku ma'abota ilimi da fikira.

Zanyi magana ne kan yadda yan uwa na mata suka takaita rubuce-rubucen su iya kawu kan su, basa yi mana nasiha, duba da muma muna bukata, amma sai suka karkatar da alqaluman su isu-isu. ko menene hikimar yin hakam?

Shin, baku san tasirin ku a rayuwar mazaje bane, ko su, mazajen sun sa karatu da kuma nasihohi ne har ya ishe su? Ni inaga kune kuke da damar yi mana nasiha kuma muyi saurin fahimta, duba da cewa; akalar mu da komi namu mukan mika shi ne zuwa gare ku.

Kuyi amfani da tasirin ku wajen tjnasar damu idan muka kaucewa tafarki, mata ta tunatar da miji, budurwa ta tunasar da saurayi, haka ma Sister a kafar sadarwa ta lizimci yiwa friend din ta nasiha, amma sai abin ya tsaya kawai ga iya kawu kan su.

shin, ko kuna rayuwa ne ku kadai a dukkan wuraren rayuwar ku, ina nufin gidajen mazajen ku, iyayen ku, da shafinan ku na kafafen sadarwa? In kuka duba zaku ga kuna tare ne hade maza da mata, masu tunanuna da ra'ayoyi ma banabanta. wannan dama ce ta isar da sakon addini cikin sauki.

Misali: Da Yawan susters sunfi rubutu kan hijabi, matsalolin zamantakewar su da samari, da matsalolin zaman aure. shin, anan bakwa mu'amala da maza ne koko kuna soyayya ne a junan ku mata? Kunga wannan sassaukar amsa zaku bada anan cewa; mafi ma yawan wadannan abubuwan kuna yin su ne don mazajen.

To, Lallai bai kamata a ware su a dukkan lamurra ba, kamar yadda muke rayuwa tare, to a komi ma ba'a ware wani bangare. Fatan Yan uwa na mata zasuyi amfani da wannan damar da suke dashi kan samarin mu, wajen saita tunanin su kan bin hanyar addini mikakkiya.


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post