Gamayyar kungiyoyin Arewa (CGN) karkashin jagorancin Nastura Ashir Sharif, ta bayyana cewa za ta fara gudanar da zanga-zanga a fadin Arewacin Nijeriya domin kira da babbar murya ga gwamnatin Muhammadu Buhari da ta kawo karshen kashe-kashen rayukan al'umma, garkuwa da mutane, hare-haren ta'addanci da kuma Boko Haram a yankin Arewa.
Zanga-zangar mai taken # EndInsecurityNow za ta fara gudana ne a gobe Alhamis 15 ga watan Oktoba 2020 a dukkan jihohin Arewacin Nijeriya.
Don haka wannan kungiya ta i kira ga duk wani dan Arewa mai kishin kawo karshen ta'addanci da kashe-kashen rayukan al'umma ya fara rubuce-rubuce a kafafen sada zumuntar zamani yana kiraye-kiraye ga gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro a yankin Arewa da Hashtag
# EndInsecurityNow .