Ƙungiyar da ke sa ido kan ayyukan gwamnati a Najeriya mai suna Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta kai ƙarar gwamnatin Najeriya wurin mai shigar da ƙara a kotun hukunta manyan laifuka.
Ƙungiyar na neman kotun ta binciki rahotannin da ke cewa “jami’an tsaro da ‘yan siyasa sun yi amfani da ‘yan daba domin cin zarafin masu zanga-zangar EndSARS a Abuja da Legas da Osun da Kano”.
SERAP ta roƙi Fatou Bensouda ta ƙoƙarta wurin “tabbatar da cewa an gurfanar da masu laifi waɗanda akasarinsu jami’an gwamnati ne da sojoji da ‘yan siyasa da suka shiga lamarin kai-tsaye ko ta hanyar wakilci”.
Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta ce an kashe aƙalla ‘yan zanga-zangar EndSARS 38 a faɗin Najeriya, inda aka kashe mutum 12 a Legas ranar Talata bayan sojoji sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar.