Dukkan Mumini Na Tsoron Haduwar Sa Da Ubangijin Sa, Har Lokacin Zuwan Mala'ikan Mutuwa !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

 WADANDA HAQQINSU YAFI NA MAHAIFANMU A KANMU 

A koda yaushe mumini cikin fargabar haduwa da Ubangijinsa yake, wanda hakan ke sa shi qara neman kusaci gare shi da kuma aikata abinda zai nisantar da shi daga fushin Ubangiji. 

Shi kuwa fajiri cikin nishadi yake wanda hakan ke sanya shi ya mance da haduwa da Ubangiji, ba zai gane wannan kuren nasa ba har sai lokacin da Mala'ikan mutuwa yazo masa. 

Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 

قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ لَا يَزَالُ الْمُؤْمِنُ خَائِفاً مِنْ سُوءِ الْعَاقِبَةِ وَ لَا يَتَيَقَّنُ الْوُصُولَ إِلَى رِضْوَانِ اللَّهِ حَتَّى يَكُونَ وَقْتُ نَزْعِ رُوحِهِ وَ ظُهُورِ مَلَكِ الْمَوْتِ لَهُ.

" MUMINI BA ZAI GUSHE BA YANA MAI TSORON MUMMUNAN QARSHE, KUMA BA ZAI SAMI YAQININ SAMUN YARDAR ALLAH BA HAR SAI LOKACIN ZARE RUHINSA DA KUMA BAYYANAR MALA'IKAN MUTUWA GARE SHI ."

Allah (T) ya bayyanar mana yadda siffar Mala'iku ke kasancewa ga mutum yayin mutuwa, Idan mumini ne sukan zo masa da siffa mai kyau, kuma su zare ransa cikin nishadi. Idan haka ta kasance gare shi sai ya sami yaqinin cewa ya sami yardar Allah. 

Shi kuma fajiri sukan zo masa ne da mummuniyar siffa ta tsoratarwa tare da saukar ransa cikin tsanani. 

SHAGALTUWA WAJEN BAUTAR ALLAH 

Manzon Allah (S. A. W. W) na cewa; 

 قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ مَنْ شَغَلَتْهُ عِبَادَةُ اللَّهِ عَنْ مَسْأَلَتِهِ أَعْطَاهُ أَفْضَلَ مَا يُعْطِي السَّائِلِينَ.

" DUK WANDA BAUTAR ALLAH TA SHAGALTAR DA SHI AKAN WASU MAS'ALOLINSA (na qashin kansa) ZA A BASHI MAFIFICIN ABINDA ZA A BAIWA MASU ROQO. "

Umarni Allah ne da kuma alqawarinsa cewa mu roqe shi zai bamu. To, Idan muka shagalta da bauta masa fiye da yadda muka damu da al'amarin duniyarmu, sai bamu alkhairori masu yawa fiye da yadda zai bawa wadanda suka roqe shi. 

    NI'IMA MAFI GIRMA 

Imam Sadiq (A. S) na cewa; 

وَ قَالَ الصَّادِقُ ع‏ مَا أَنْعَمَ اللَّهُ عَلَى عَبْدٍ أَجَلَّ مِنْ أَنْ يَكُونَ فِي قَلْبِهِ مَعَ اللَّهِ غَيْرُهُ.

" BABU WATA NI'IMA MAFI 'DAUKAKA GA BAWA FIYE DA YA KASANCE BABU WANI CIKIN ZUCIYARSA KOMA BAYAN ALLAH ."

Duk wanda ya kasance Allah ne cikin zuciyarsa ba wani ba, to, ya sami babbar ni'imar da babu kamarta.

IYAYE MAFIYA GIRMA GARE MU 

Manzon Allah (S.A.W.W) na cewa; 

قَالَ الْإِمَامُ ع قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ أَفْضَلُ وَالِدَيْكُمْ وَ أَحَقُّهُمَا بِشُكْرِكُمْ مُحَمَّدٌ وَ عَلِيٌّ.

" MAFIFITA MAHAIFANKU KUMA WADANDA SUKA FI CANCANTA KU GODE MUSU SUNE MUHAMMAD DA ALIYU ."

Wannan hadisi na nuna mana ne cewa Manzon Allah da Imam Ali abu guda ne wajen girman haqqinsu a kanmu, abinda ya bambanta su kawai shine manzanci. 

WADANDA SUKA FI KOWA HAQQI A KANMU 

Daga Imam Ali (A. S), daga Manzon Allah (S. A. W. W) 

. وَ قَالَ عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ ع سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ ص يَقُولُ‏ أَنَا وَ عَلِيٌّ أَبَوَا هَذِهِ الْأُمَّةِ وَ لَحَقُّنَا عَلَيْهِمْ أَعْظَمُ مِنْ حَقِّ أَبَوَيْ وِلَادَتِهِمْ فَإِنَّا نُنْقِذُهُمْ إِنْ أَطَاعُونَا مِنَ النَّارِ إِلَى دَارِ الْقَرَارِ ............

" NI DA ALIYU UBANNIN WANNAN AL'UMMAR CE, KUMA HAQQINMU A KANSU YAFI HAQQIN IYAYEN DA SUKA HAIFE SU , DOMIN MUNE MASU TSERATAR DASU DAGA WUTA ZUWA GIDAN TABBATA MATUQAR SUN YI MANA BIYAYYA........."

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏66، ص: 344

Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

        08126385470


2nd October, 2020/ 15th Safar, 1442.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post