@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KAICON KU MASU QWATAR JAGORANCI
Al'amarin shugabanci abu ne mai girman gaske kuma mai hadari ga wanda ya nema ba tare da an ba shi ba.
Rashin rabon lahira ko son duniya ne ke sa kaga mutum na neman shugabanci . Ba zai zama laifi ba ga mutum ya karbi jagoranci ko shugabanci Idan aka ba shi bisa ganin cancantarsa, domin Allah zai zame masa jagora wajen gudanarwa.
Amma idan ya kasance shine ya nema har yana yiwa mutane alqawarin cewa in suka zabe shi har ya zama shugaba zai yi musu adalci . To, idan ya kasance haka sai ka ga abinda ba a so daga gare shi, masu qwacen jagoranci abin misali ne, haka kuma wannan da ke jagorantar ku (BUHARI).
Ya zo cikin Babi dake magana kan hani game da neman shugabanci da kuma barin wilaya idan ba shi aka bawa ba ko kuma ba a buqatu zuwa gare shi ba.
81 - باب النهي عن سؤال الإمارة واختيار ترك الولايات إذا لَمْ يتعين عليه أَوْ تَدْعُ حاجة إِلَيْهِ
Abu Zarr ya bada labari daga Manzon Allah (S. A. W. W) cewa ya ce,
حديث رقم :673
وعن أَبي ذرٍّ رضي الله عنه قَالَ:
قَالَ رسول الله صلى الله عليه وسلم: (يَا أَبَا ذَرٍّ، إنِّي أرَاكَ ضَعِيفاً، وَإنِّي أُحِبُّ لَكَ مَا أُحِبُّ لِنَفْسِي. لاَ تَأمَّرَنَّ عَلَى اثْنَيْنِ، وَلاَ تَوَلَّيَنَّ مَالَ يَتِيمٍ)
" YAA ABU ZARR ! LALLE NI INA GANINKA RARRAUNA , KUMA NI INA SO MAKA ABINDA NAKE SOWA KAINA . KADA KAYI SHUGABANCI AKAN MUTUM BIYU , KUMA KADA KA JIBINCI DUKIYAR MARAYA. "
(رواه مسلم)
Sannan an samo cikin wani hadisi wanda Abu Huraira ya bada labarinsa daga Manzon Allah (S. A. W. W) cewa,
حديث رقم :675
وعن أَبي هريرة رضي الله عنه:
أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلم قَالَ: (إنَّكُمْ سَتَحْرِصُونَ عَلَى الإمَارَةِ، وَسَتَكونُ نَدَامَةً يَوْمَ القِيَامَةِ)
" LALLE KU DA SANNU ZA KUYI KWADAYIN SHUGABANCI, KUMA DA SANNU ZAI ZAME MUKU NADAMA RANAR ALQIYAMA. "
رواه البخاري
(RIYADUS-SAALIHEEN)
Saboda haka duk wadanda suka yi qwacen jagoranci a zamanin baya da masu neman mulki na wannan zamani za suyi nadama ranar alqiyama.
Ita nadamar ranar alqiyama kuwa ba ta da amfani, domin ba za a dawo duniya a gyara kuren abinda aka aikata ba, kuma ba a karbar uzurinsu ko da sun kawo.
DON HAKA KADA KUCE AI WANE KIRANSA AKAYI BA SHI YA NUNA YANA SO BA.
Domin a magabata asalan sunyi zama kan haka yayin da suka ji Annabi Muhammad (S. A. W. W) ya nasabtar da Imam Ali (A. S) a Ghadeer-Khuum.
Su kuma na yanzu dasu ake bi gari-gari jiha-jiha ana yin alqaqura cewa in an zabe su za su cika musu.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda.
08126385470
27th October, 2020/ 10th Rabi'ul-Awwal, 1442.