*- Abdullahi Isah Wasagu*
*ZUWA GA 'YAN UWA:
- Gwangilar hukumar Facebook kan 'yan uwa almajiran Malam Zakzaky game da isar da sakon zaluncinsu a shafin Facebook.
Wannan wani dan takaitaccen rubutu ne na gaggawa game da yadda hukumar gudanarwar Facebook ke kullema 'yan uwa almajiran Malam Zakzaky shafukansu na Facebook.
Wato muna zargin gwamnatin Najeriya ta hada hannu da hukumar Facebook din ne, domin takaita yadda almajiran Malam Zakzaky ke isar da sakonnin hotuna, bidiyoyi da kuma rubuce-ribuce na barnar da suka yi a Zaria a 2015, kuma suke ci gaba da yi, gami da ci gaba da rike Malam Zakzaky bayan hukuncin babban Kotun tarayya da ta wanke shi daga dukkan wani zargi; ta kuma bada umarni a sake shi, amma sun yi biris da umarnin saboda ci gaba da kokarin cinma wasu muggan muradunsu.
Muna kyautata zarginmu ne da wani rahoto da kafafen yada labarai suka fitar kwanakin baya, wadda hukumar kula da kafafen sadarwa (communications) ta kasa ta fitar cewa, cikin watan Oktoban nan da muke ciki ko Nuwanba mai zuwa za su kaddamar da bangaren da zai kula da yadda 'yan kasa ke cin karensu ba babbaka a shafukan sada zumuta na zamani, da suka had a da zagi da cin zarafin shuwagabanni da kuma masu kima da daraja a idanun 'yan kasa, kamar yadda suka ambata cikin harshen Turanci.
Daga kwanaki 5 baya zuwa yau Asabar 4/10/2020, su kullema 'yan uwa shafukansu da dama.
Sannan suna ci gaba da kullewa. Ciki harda ni, sun kullemin shafuka guda biyar, ciki harda manyan shafuka da ake kira "Page" mai dauke da 'followers' da 'Likers' sama da 11, 000.
Babu raba daya biyu, kwangila ce daga gwamnatin Najeriya.
TSOHON POLICY NA FACEBOOK:
1- Duk wadanda suka rage ba a kulle ba, kuma suna ci gaba da isar da sakon harka Islamiyyah, to su kiyaye wasu ka'idoji guda biyu ta janibin saka hotuna da kuma sharing.
Wato a dan takaitaccen binciken da na yi, tun kusan shekara 2 baya, yana daga cikin Policy dinsu kada a saka hotuna da suka wuce guda 5.
Kada a yi tagging din mutane da suka wuce mutane 13.
Kada a yi sharing a groups da suka wuce 10 .
Wannan Policy dinsu ne fiye da shekaru 2.
SABON POLICY DINSU NA YANZU :
- Duk wandanda aka kullema account suka sake bude wani, to yana da kyau su lura da wadan nan abubuwa, idan ba haka ba, to idan za ka bude sau 20; to za su kulle sau 20:
1- Ya zama wajibi idan ka bude sabon Facebook account yanzu, kada ka tura Friend Request ma wanda baka da nombar wayarsa, haka shima bashi da nombar wayarka. Dole ne wanda za ka turama Friend Request ya zama kuna da nombobin juna, ta haka kuka cika terms and conditions/policy na shafin Facebook na yanzu.
2- Idan ka kuskura ka tura Friend Request na wanda ba ku da nombobin juna, za su kullema account.
3- Kada ka sake ta tura otomatic(authomatic) Friend Request da Facebook ke turoma da kansu, da zarar ka bude sabon facebook din. Suna turoma, ka yi disagreeing dinsu, ka tura da kanka(kuma wanda ka ke da numbarsa yake da naka).
4- Kada ka turo Friend Request da suke wuce guda 5 a lokaci guda. In so samu ne, kada su wuce guda 4, bayan ka samu wasu 'yan awowi, sai ka sake tura turama mutum 4 ko 5(wadanda kuke da nombobin juna).
5- Haka za ka bi wadan nan matakan har sai ka yi watannin 3. A yayin da ka shiga watanni na 4, za ka iya turama kowo Friend Request, amma kada su wuce mutane 5 a lokaci guda.
A yayin da ka bude sabo, za ka iya ka yita updating Profile Picture lokaci-bayan-lokaci, domin ta hake ne, mutane za su ganka a newsfeed, su rika turoma Friend Request. Kada a rika updating da hotuna masu alamin Harka Islamiyyah ko su Malam(H).
6- Idan sabon Accout ne, kada ka cika yin Like ko Sharing da suka wuce kimanin 5, 7, zuwa 10. Idan ka cika sharing ko Like da yawa a lokaci daya, za su kulle in dai sabon account ne.
Sai bayan watanni 3 zuwa 4 za ka sake jiki ka yi komai.
MASU TSOFAFFIN ACCOUNT DA MA SABBI:
1- A kiyaye saka hotuna da yawa. Idan so samu ne, kada ka saka hotuna da suke wuce guda 3 ko 4. Idan sun yi yawa sosai , su kai guda 5. Kana saka hotunan da suka wuce ka'ida, za su iya kullema accout.
2- Kada ka yi tagging kowa a Post dinka. Idan za ka yi tagging, kada su wuce limit na Facebook tagging, wato guda 13. Idan so samu ne, kada ka yi tagging ko daya.
3- Sannan kada kayi amfani da abusive words(kalmomin cin mutunci) wato kamar Allah ya tsinema wane, Criminal wane, da ta'adda wane da sauransu. Yanzu sun yi installing din abusive words in many langauges(kamar yadda suka yi intalling din wasu kebatattun kalmomi wadanda ba za ka iya bude account da su ba, sai dai sunan yanka, wato Proper Nouns). Idan ka cika amfani da abusive words, za su kullema account.
Insha Allah, idan aka kiyaye wadan nan, to zai zamana an samu sauki, sai dai kuma idan abin ya tashi daga sada zumunta na ra'ayi ba tare da cin mutuncin wani ba(Kamar yadda suka amshi gwangilar saka hoton Shaheed Sulaimani na Iran, suka rika kulle accounts din da suka saka hoton Gen. Sulaimani).
BABIN SHAWARA:
Lallai a tunanina, da kuma babin shawara irin ta dan karamin hankalina, lallai ya zama wajibinmu, mu sake zage tumazaginmu mu dauki damarar isar da sakonnin wannan Harka a Facebook. Allah ke yi ba mutum ba, amma fa mu sani, wadanda ba su da zurfin Ilimin Boko; kuma basu damu sa social media sosai ba; to sun fi yin Facebook a kan Twitter.
Don haka, idan muka bar Facebook, to za ai ta yi mana abubuwa, duniya bata san an yi mana ba. Tun kafanonin sadarwa sukan saka labaranmu ne , a wasu lokuta, ba koda yaushe ba.
- To shawara a nan shi ne, ya zama dole mu samu nizami. A kowace da'ira, a samu ayyanannun blogs ko websites wadanda za a rika kula da su officially da kuma mutum daya ko biyu koma dai wani irin tsari ne, wadanda za su rika updating din programs na Harka. Kuma ya zama bisa nizamin da'ira da kuma Harka din.
- Ya zama sauran ba'adin 'yan uwa masu ta'ammuni da Facebook din su rika, like ko sharing ko comment a blogs ko websites din, domin karfafa blogs din su yi kwari sosai, har su zama kamar na sauran kafafen sadarwa na kudi.
- Kada dan uwa ya damu dole sai ya zama marubuci ko an rika jin sunansa, ka zama mai bada taka gudunmawar a yayin da Writters na blogs dinmu ko Websites suka yi updating blogs ko websites. Ya zama kar ka wuce sai ka yi Like, a wasu lokutan sharing.
Kada sauran 'yan uwa su damu sai sun yi magana suna zagi ko cin mutuncin su Buhari, saboda kaucewa dakileka da Facebook din za su na wajen yin Like ko Share ko Comment, ya zama kaima ka taimaka. Da zarar suka kullema accout, to sun ci nasara ne a kanka, ya kamata kuma kai kaci nasara ne a kansu wajen kaucewa kulleka din.
Daga karshe:
Yana da gayar muhimmanci a samar da nizami wajen karfafa blogs din nan a da'irance(Officially) sannan ya zama sauran ba'adin 'yan uwa an kasu biyu ne.
1- Masu update
2- Da masu taimakama updates din ta yin comment, share, like.
Lallai ci gaba da zama individually, to za fa su ci gaba da rufe mana shafuka ne. Tunda sun lura activities dinmu yana making influence a diniyar Facebook din.
Insha Allah. Allah ya daura gaskiya bisa karya, ya bawa al'ummar kasar nan iko da fikiran gane gaskiya a duk inda take.
Abdullahi Isah Wasagu
4/10/2020.
Don Allah a yi sharing dinsa sosai domin sakon ya isa ga 'yan uwa.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com