DAGA KALAMAN HIKIMA NA IMAM ALI (A. S)! Babu 'Daukaka Wacce Tafi Tsoron Allah !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @



من أقوال الإمام علي عليه السلام :



Ya zo cikin zantukansa (A. S) inda yake cewa, 



 التُّقى رئيس الأخلاق


" TAQAWA (tsoron Allah) ITA CE KAN KYAWAWAN 'DABI'U ."


A yanayin halittar thaqalain (mutum da aljan) an yi su ne dauke da kai (head), da zarar an rasa shi to, babu gangan jiki, domin ba za ta rayu ba dole sai da shi. 


Saboda haka duk wanda ka same shi da tsoron Allah za kaga kyawawan dabi'u tare da shi. Kuma wanda ka gan shi da kyawawan dabi'u za ka tarar da shi mai imani ne, domin tare suke tafiya. 


Idan ka rasa daya daga ciki taqawa/kai za ka rasa dayan ma. 



A wani guri kuma yake cewa, 


 لا شرف أعلى من التقوى


" BABU WATA 'DAUKAKA WACCE TA KE SAMA DA TAQAWA ."


Duk girman mutum ko karatunsa ko dukiyarsa ko kuma mulkinsa matuqar ya rasa taqawa, to, babu wata daukaka gare shi. 


Amma duk talaucin mutum ko rashin lafiyarsa matuqar yana da tsoron Allah (taqawa), to, wannan mutumi shine madaukaki kan kowa a wajen Allah. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


          08137925034


27th October, 2020/ 11th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post