Daga Cikin Abinda Allah Ya Fadawa Musa (A.S) Yayin Ganawar Su: Babu Mai Son Allah Na Gaskiya, Sai Mai Raya Dare Da Ibadu !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


BABU MAI SON ALLAH NA GASKIYA SAI MAI RAYA DARE DA IBADA 


Wato shi son Allah ba a baki yake ba dole sai yayi mudabaqa da ayyuka. Duk wanda yace yana son Allah amma ba ya kusantarsa cikin dare da ibada ka kira shi cikakken maqaryaci. 


Tashin cikin dare don yin ibada na daga cikin abinda ke gaskata soyayyar mutum ga Mahalicinsa. 


Wannan na daga cikin abinda ya bambanta Sayyid Zakzaky (H) da sauran masu qaryar son Allah a bakunansu. Shi ya kasance bawa mai yawan kusantar Allah cikin dare da yawan azumi da rana. 


Su kuwa sauran malaman sunyi hannun riga da aikata ayyukan neman kusanci ga Allah. Na'am, na sani cewa su ma ba sa iya yin bacci sosai cikin dare, sai dai rashin baccin nasu na da alaqa ne da tunanin ta ina za su bullowa mabiyansu don su sami kudi da daukaka wajensu da kuma neman samun yarda cikin fadar azzalumai. 


Yazo cikin riwaya wacce ta tuqe kan Abu Abdullahi (A.S) yace; 


لي، الأمالي للصدوق أَبِي عَنْ سَعْدٍ عَنِ ابْنِ أَبِي الْخَطَّابِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنِ الْمُفَضَّلِ عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ:


 كَانَ فِيمَا نَاجَى اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ بِهِ مُوسَى بْنَ عِمْرَانَ ع أَنْ قَالَ لَهُ يَا ابْنَ عِمْرَانَ كَذَبَ مَنْ زَعَمَ أَنَّهُ يُحِبُّنِي فَإِذَا جَنَّهُ اللَّيْلُ نَامَ عَنِّي أَ لَيْسَ كُلُّ مُحِبٍّ يُحِبُّ خَلْوَةَ حَبِيبِهِ هَا أَنَا ذَا يَا ابْنَ عِمْرَانَ‏[12] مُطَّلِعٌ عَلَى أَحِبَّائِي إِذَا جَنَّهُمُ اللَّيْلُ حَوَّلْتُ أَبْصَارَهُمْ مِنْ قُلُوبِهِمْ وَ مَثَّلْتُ عُقُوبَتِي‏


" Ya kasance daga cikin abinda Allah (T) ya gana da Musa dan Imrana (A. S) yace masa; 


" YAA 'DAN IMRANA, YAYI QARYA DUK WANDA KE RIYAWA CEWA YANA SO NA, IDAN DARE YA LULLUBE SHI YAI YAYI MIN BACCI. ASHE BA KOWANNE MASOYI YANA SON KEBEWA DA MASOYINSA BANE ?


TO 'DAN IMRANA! NI NAN INA KALLON (dukkan) MASOYANA IDAN DARE YA LULLUBE SU IDANUWANSU NA JUYAWA DAGA ZUKATANSU , KUMA SU RIQA MISALTA UQUBATA (cikin zukatan nasu) ."


__________________________


(2) أمالي الصدوق ص 219.


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏67، ص: 15


Saboda haka duk wanda ke bijiro da azabar Allah cikin zuciyarsa ba zai iya kwantawa cikin dare yana sharar baccinsa ba tare da ya miqe don ganawa da Mahalicinsa ba. 


Shi yasa a koda yaushe Sayyid Zakzaky (H) ke umartarmu da raya dare kuma yake koyar damu a aikace. 


Alhamdulil-Lah, wannan koyarwar tasa ta tasirantu cikin 'yan'uwa da dama, domin ko da wani programme aka shirya wanda za kwana za ka ji ana umartan 'yan'uwa da suzo da kayan addu'o'insu da Qur'anansu don raya dare da ibada. 


" KUMA DAGA CIKIN DARE KAYI QOQARI DASHI (Qur'ani wajen raya daren) QARI NE GARE KA (koma bayan ayyukan wajibai). LALLE TASHIN DARE SHINE MAFI TSANANIN NUTSUWA KUMA MAFI DAIDAITO GA MAGANA ."


               (Qur'an) 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


(08126385470-08137925034)


21st October, 2020/ 4th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post