Da yake jawabin da yasaba gabatarwa na pre-khudba duk bayan idar da sallar Juma'a a Masallacin Fagge, wakilin yan'uwa Musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (h) na da'irar Kano da kewaye Sheikh Dr. Sunusi Abdulkadir ya bayyana da'awar Sayyid Zakzaky a matsayin iri daya da da'awar Shehu Mujaddadi Usmanu dan Fodiyo.
Shehin Malamin yayi dogon bayani game da rayuwar Shehu Usmanu dan Fodiyo wanda ake bukukuwan tunawa dashi a wannan wata, inda a wani bangare na jawabinsa yake cewa *Wani zai iya tambaya yace mu ai abin da muke iya gani na sarakunan gargajiya wayanda ake cemasu magadan Shehu, to aimu ba Musulunci muke gani dari bisa dari ba, sai muce maka e abin da ya faru shine bayan Shehune sai wasu daga cikin almajiran Shehu suka chanza. Menene abin mamaki in ance maka almajiran Shehu sun chanza Sahabban Manzon Allah ma aka sami wayanda suka chanza ko baka lura ba.
Ba mamaki idan an sami almajiran Shehu wayansu sun chanza kamar yanda za a iya samun almajiran Sayyid Zakzaky wayansu su canza ko baka haka ba. Saboda haka ba wani abin mamaki wannan zahirace tabbatacciya a Alkur'ani da Sunna cewa dan Adam yana chanzawa. Mutum yana chanzawa shi yasa aka bamu addu'ar ''Ya mukalibal kulubi sabbit kalbi ala dinika''. Shi yasa aka bamu addu'ar nan da Sayyid Zakzaky ya bamu wacce ake yawan karantata wato musamman a lokacin gaibar sahibil asr wa zaman ''ya Allahu ya rahman ya rahimu ya mukalibul kulub.... addu'a ce idan mutum yana yawan karantata Allah zai tabbatar dashi akan shiriya bazai sami zamewa ba, bazai sami kaucewa ba. Wannan shine Shehu Usmanu dan Fodiyo daga bayane wasu daga almajiransa suka canza sai suka mayar da tsarin da yazo dashi na Musulunci ya zama sarautar gargajiya. Kuma wannan ba lefin Shehu bane, shi yayi nasa aikin ko ba haka ba ( Wama alal rasulu illal balag) shi ya isar da sako ya koyar da mutane tsarin Musulunci ya dorasu akan tafarki. Amma daga baya sai wayansu suka kukkushe suka lalace suka watsar da wannan koyarwar ta Musulunci saboda wani abu, Allah ya kiyashemu.
Tambaya ai hakane da'awar nan ta Allama Sayyid Zakzaky haka ta faro dama da'awar Shehu Usmanu ce, irin ta Shehu Usmanu ce, to amma daga baya kuma munga kun canja, kun koma Shi'a, wani bazai fadi haka ba, wasu suna fadin haka ko? Amsa da'awar Shehu Usman dan Fodiyo dan'uwa da'awar Musulunci ce, ba da'awar mazahaba bace Shehu Usmanu da'awarsa dan Kadiriyya ne amma ba da'awar Kadiriyanci yayi ba, Shehu Usmanu ba da'awar Malikiya yayi ba, du da dan Mazahabin Malikiya ne a fikihu. Shehu Usmanu dan Fodiyo mabiyin mazahabin Ahlul baiti ne, rubuce-rubucensa sun nuna sheda, amma baiyi da'awa izuwa Shi'anci ba. Ba da'awar Mazahaba yayi ba.
Saboda haka Allama Sayyid Ibrahimul Zakzaky shima da'awarsa Islamiyya ce, irin ta Shehu ce dan Fodiyo sak.
Shiyasa sai kaga da'awar kamar wato ainihin Malikiya-Malikiya saboda akwai yan Malikiya a cikinmu, sai ka ganmu Sufaye-Sufaye soboda akwai Sufaye a cikinmu, sai ka ganmu yan Shi'a-Shi'a saboda akwai yan Shi'a a cikinmu. Amma uwa uba tushe shine Musulunci shine kalmar nan ta La'ilaha illallahu Muhammad rasulullahi. Wacce da'awace tafi da'awar Musulunci. Wasu suna damuwa wai sai ayi da'awar bangarenci ko muce mu yan Kadiriya ne wallahi Kadiriya za ayi, ko muce mu yan tijjaniya ne billahillazi tijjaniya za ayi, ko muce mu yan Malikiya ne inba Malikiya ba sai dai a mutu, ko muce mu yan Jafariyane inba Jafariya ba kowa ya tarwatse.
A'a Malam da'awar ta Musulunci ce. Yau inda zamuce da'awar mu ta Shi'anci ce, to da kaga taimako wajen gwamnatin Nigeriya. Ai anmana wannan tayinma in baku sani ba cewa mu tsaya muyi Shi'ancinmu kawai, mudaina cewa Musulunci, mu daina cewa anayin zalunci, mu daina cewa a koma tafarkin Manzon Allah mu tsaya muyi Shi'anci kawai, muyi Ashuranmu, musa bakar rigarmu zasu gina mana Hussainiyya. Duk inda mukeso mu fada za a gina mana Hussainiyya tangamemiya muyi ta Ashura muna dukan kirji muna kuka. Amma kar muce ana zalunci, kar muce ayi tsarin Musulunci.
Mukace anki Musulunci za ayi, wanda zaiyi Shi'a yayi Shi'anci sa, wanda zaiyi sufanci yayi sufancinsa, wanda zaiyi Jafariya yayi Jafariyarsa, wanda zaiyi Malikiya yayi Malikiyarsa. Duk abin da kaga ka fahimta a Musulunci kayi kayanka, tushen menene shine Musulunci.
To wannan shine da'awar Shehu Usmanu dan Fodiyo kuma akanta Mal Zakzaky yake, don Allah an canza kenan? ba a canza ba. 'Labbaika dan Fodiyo!'.
Bayan jawabin dan Fodiyo Dr. Sunusi Abdulkadir ya tabo batun haihuwa gwarzon matashin nan Sayyid Ahmad dan gidan Allama Sayyid Zakzaky inda ya bayyana shi a matsayin samfur kuma gwarzo wanda baza a taba mantawa dashi ba, ya kuma fassara mana yanda Allama Sayyid Ibrahimul Zakzaky yakeso mu zama a aikace.
Sannan a karshe ya rufe jawabunsa na wannan rana da batun Wafatin Manzon Allah (S) wanda ya kasance a wannan wata na Safar, inda ya bayyana cewa Manzon Allah Shahada yayi duba da irin ruwayoyin da suka tabbatar da cewa Shahada yayi.
Daga Yusuf Nadabo (Baban Sayyid)