DA MENE ZAMUYI ALFAHARI: Mu ana so muyi Alfahari da kisan kare dangi da bature yayi ma kakannin mu ne, Ko kuma zamuyi Alfahari da rushe daular musulunci ta Shehu Fodiye?



Na bibiyi kafafan sada zumunta amma abinda na lura da yawa 'yan najeriya suna korafi dangane da bikin cikar najeriya shekaru sittin bisa dalilan matsin rayuwa, mugayen shugabanni, rashin tsaro, da dai ire iren wadannan.


Ashe da ana shan jar miya ne za'ayi ta murna ne ko?


Lallai Turawa Sun Cuce Mu!!!

Tom bari kuji kuma kuce na fada muku!!!


Duk Al'ummar da ta rasa tarihin kashin kanta wanda zatayi Alfahari dashi kuma ta raini 'yan baya domin kishin kasa tom wannan al'ummar ita da ci gaba sai dai ta jiyo a kasashen ketare.


Mu ana so muyi Alfahari da kisan kare dangi da bature yayi ma kakannin mu ne?

Ko kuma dalar gawarwakin kakannin mu da bature yayi?

Ko kuma zamuyi Alfahari da rushe daular musulunci ta shehu fodiye?

Ko zamuyi Alfahari da auren Ala tsine da bature ya hada mu da wadanda muka saba dasu ta kowanne bangare na al'ada addini dama yanayin zamantakewa?

Zamuyi Alfahari ne da 'yancin zahiri da aka sawwala an bamu wanda dashi gwamma a zauna a yadda ake da can tunda yanzu ba'a bama kowa shugabancin mu sai an zabo mugayen cikin mu.


Ni ina tausaya mana yadda mukayi saurin mance kawunan mu.

Diyan Shehu Dan Fodiye Muke, Ko Mun Mance Shi Bature Bai Mance Ba!!!
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post