Da Kuna 'Daukar Abinda Sayyid Zakzaky (H) Ke Fada Da Bazaku Shiga Rudani Ba !!!


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


A IRIN WANNAN HALI SU ABUBAKAR SUKA SAMI KANSU CIKI 


Al'amarin biyayya ga jagora abu ne mai girman gaske wanda mai rabo kadai ke samun dacewa cikinsa. Ba za ka taba samun dace wajen Allah ba har sai ka kasance mai dauka da kuma aiki da abinda kake ji daga jagora. 


Sayyid Zakzaky (H) jagora ne na gaskiya wanda biyayya gare shi tamkar biyayya ga fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W) ne. Mabiyansa sun kasance tamkar Sahabban Annabi (S. A. W. W) yadda ake samun masu tsananin riqo da koyarwarsa da kuma masu shagala cikin al'amarin duniya da mata da dukiya. 


Rashin dauka da kuma aiki da abinda Sayyid Zakzaky (H) ke karantarwa yasa ake samun sabani cikin 'yan'uwa maza da mata (brothers and sisters). Wannan kuwa abu ne a sarari wanda kowa ya sani, domin za ka samu 'yan'uwa na tattauna irin wannan matsalar da kuma zargin kansu-da-kansu, ko da kuwa ba za su iya gyarawa ba. 


To, irin wannan ta faru cikin Sahabban Annabi Muhammad (S. A. W. W) irin su Abubakar da Hamzalata dama wasu da dama , har takai suna zargin kansu-da-kansu kan wannan al'amari. Kamar hakane 'yan'uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) suke a halin yanzu. 


Ya zo cikin Riyadus-Saliheen na Imamun-Nawawi cikin Babin taqaitawa cikin ibada yadda Abubakar ya zargi kansa cewa ba ya aiki da dukkan abinda yaji daga Manzon Allah (S. A. W. W). 


Ga dai riwayar kamar haka, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


14 - باب في الاقتصاد في العبادة


 حديث رقم :151


وعن أبي رِبعِي حنظلة بنِ الربيعِ الأُسَيِّدِيِّ الكاتب أحدِ كتّاب رَسُول الله صلى الله عليه وسلم، قَالَ: 


لَقِيَنِي أَبُو بَكر رضي الله عنه، فَقَالَ: كَيْفَ أنْتَ يَا حنْظَلَةُ؟ قُلْتُ: نَافَقَ حَنْظَلَةُ! قَالَ: سُبْحَانَ الله مَا تَقُولُ؟! قُلْتُ: نَكُونُ عِنْدَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم يُذَكِّرُنَا بالجَنَّةِ وَالنَّارِ كأنَّا رَأيَ عَيْنٍ (1)، فإِذَا خَرَجْنَا مِنْ عِنْدِ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم عَافَسْنَا الأَزْواجَ وَالأَوْلاَدَ وَالضَّيْعَاتِ نَسينَا كَثِيراً، قَالَ أَبُو بكر رضي الله عنه: فَوَالله إنَّا لَنَلْقَى مِثْلَ هَذَا، فانْطَلَقْتُ أَنَا وأبُو بَكْر حَتَّى دَخَلْنَا عَلَى رَسُول الله صلى الله عليه وسلم. فقُلْتُ: نَافَقَ حَنْظَلَةُ يَا رَسُول اللهِ! فَقَالَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم: (وَمَا ذَاكَ؟) قُلْتُ: يَا رَسُول اللهِ، نَكُونُ عِنْدَكَ تُذَكِّرُنَا بِالنَّارِ والجَنَّةِ كأنَّا رَأيَ العَيْن فإِذَا خَرَجْنَا مِنْ عِنْدِكَ عَافَسْنَا الأَزْواجَ وَالأَوْلاَدَ وَالضَّيْعَاتِ نَسينَا كَثِيراً. فَقَالَ رَسُول الله صلى الله عليه وسلم: (وَالَّذِي نَفْسي بِيَدِهِ، لَوْ تَدُومُونَ عَلَى مَا تَكُونونَ عِنْدِي، وَفي الذِّكْر، لصَافَحَتْكُمُ الملائِكَةُ عَلَى فُرُشِكُمْ وَفي طُرُقِكُمْ، لَكِنْ يَا حَنْظَلَةُ سَاعَةً وسَاعَةً) ثَلاَثَ مَرَات. رواه مسلم. قولُهُ: (رِبْعِيٌّ) بِكسر الراء. وَ(الأُسَيِّدِي) بضم الهمزة وفتح السين وبعدها ياء مكسورة مُشددة. وقوله: (عَافَسْنَا) هُوَ بِالعينِ والسينِ المهملتين أي : عالجنا ولاعبنا. وَ(الضَّيْعاتُ) : المعايش.ـــــــــــــــــ(1) رَأيَ عَيْنٍ : قال النووي في شرح صحيح مسلم 9/59 (2750): (أي نراها


An karbo/samo daga baban Rabi'i Hamzalata Bn Rabi'i Al-Usayyidiy, marubuci daga cikin marubutan Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" Abubakar ya hadu dani sai yace, " Ya kake yaa Hamzalata ?" Sai nace, Hamzalata yayi munafurci !" Sai (Abubakar) yace, " Tsarki ya tabbata ga Allah, me kake fada haka (ko dadin ji babu ?" Sai nace, 


" Muna kasancewa a wajen Manzon Allah yana tuna mana Aljannah da Wuta (sai muna ganinta) kamar a zahiri , amma yayin da muka fita daga wajen Manzon Allah (S. A. W. W) sai matayenmu da 'ya'yanmu da shagulgulanmu su shagaltar damu, sai mu manta (abubuwa) masu yawa (daga abinda muka ji daga gare shi ."


Sai Abubakar (R. A) yace, " AI WALLAHI MUMA MUNA HADUWA DA IRIN WANNAN (shagalar) !" 


Sai muka tashi ni da Abubakar har muka shiga wajen Manzon Allah (S. A. W. W). Sai nace, " Hamzalata yayi munafurci yaa Ma'aikin Allah. Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace, " ME KE FARUWA ! " Nace, 


" Yaa Ma'aikin Allah ! Muna kasancewa a wajenka kana tuna mana wuta da aljannah tamkar muna ganinta a zahiri (reality), amma yayin da muka fita daga wajenka sai matanmu da 'ya'yanmu da shugulgula (na duniya) su shagaltar damu, sai mu mance da yawa (daga abinda kake fada mana). Sai Manzon Allah (S. A. W. W) yace, 


" NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA ! DA ACE KUNA DAWWAMA AKAN ABINDA KE KASANCEWA A WAJENA (na abinda nake fada muku), DA KUMA TUNAWA (da abinda kuke ji daga gare ni), TO, DA MALA'IKU SUN RIQA YIN MUSAFAHA 🤝🏼 AKAN SHIMFIDUNKU (guraren kwanciyarku) DA KUMA KAN HANYOYINKU (yayin da kuke tafiya), SAI DAI YAA HAMZALATA ABIN NAKU (yin aiki da abinda nake fada muku) LOKACI-LOKACI ! "


Sau uku yake fadin haka (cewa ai lokaci-lokaci muke aiki da abinda yake fada mana ).



Imam Nawawi ya fadi haka cikin sharhin Sahihul-Muslim, Mujalladi na 9, Shafi na 59, Hadisi me lamba 2750.


Idan kuwa hakane, to, me yasa za ku riqa gani da cewa Abubakar bai cika aiki da abubuwan da yake ji daga Annabi (S. A. W. W) ba alhali ku ma haka kuke ?


Ku gyara tafiyarku, in ba haka ba kuma ku sami kanku cikin irin halin da su Abubakar suka sami kansu, wato ku kasance ayyukanku daban da abinda Sayyid Zakzaky (H) ke karantar daku. 


" WANNAN TUNATARWA CE, WANDA YASO YA RIQI TAFARKI (na kirki) ZUWA GA UBANGIJINSA ."


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 


        08126385470


30th October, 2020/ 13th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post