@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
INA KUMA GA WADANDA DAMA BASU TABA GANINSA BA ?
Ita rayuwa bata da tabbas kamar, komai kan iya canzawa ga mutum. Wani zai iya yin aikin alkhairi a farkon rayuwarsa amma sai ya canza a qarshenta.
Wani kuma kan iya aikata aikin assha, amma a qarshe sai ya canza zuwa kyakkyawa. Wani kuma yadda ya faro haka zai qare.
Saboda haka shaidar farko ga mutum ba za ta zama ita ce ta qarshe ba, dole sai ya kasance farkon nasa yazo daidai da qarshensa.
" ALLAH KAN SHAFE ABINDA YASO KUMA YANA TABBATARWA ."
(Qur'an)
Saboda haka akwai da yawa daga Sahabbai wadanda ba za su qara ganin Annabi (S. A. W. W) ba har abada domin sun canza daga abinda ya barsu akai a bayansa.
Ummus-Salamata (R. A) ta bada wannan labari cikin wannan hadisi dake biye.
Ku biyo mu don ganewa da idanuwanku.
25894- حَدَّثَنَا أَبُو مُعَاوِيَةَ ، قَالَ : حَدَّثَنَا الْأَعْمَشُ ، عَنْ شَقِيقٍ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ ، قَالَتْ : دَخَلَ عَلَيْهَا عَبْدُ الرَّحْمَنِ بْنُ عَوْفٍ ، قَالَ : فَقَالَ : يَا أُمَّهْ ، قَدْ خِفْتُ أَنْ يُهْلِكَنِي كَثْرَةُ مَالِي ، أَنَا أَكْثَرُ قُرَيْشٍ مَالًا ، قَالَتْ : يَا بُنَيَّ ، فَأَنْفِقْ ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ : " إِنَّ مِنْ أَصْحَابِي مَنْ لَا يَرَانِي بَعْدَ أَنْ أُفَارِقَهُ " , فَخَرَجَ ، فَلَقِيَ عُمَرَ ، فَأَخْبَرَهُ ، فَجَاءَ عُمَرُ ، فَدَخَلَ عَلَيْهَا ، فَقَالَ لَهَا : بِاللَّهِ مِنْهُمْ أَنَا ؟ فَقَالَتْ : لَا ، وَلَنْ أُبْلِيَ أَحَدًا بَعْدَكَ
Baban Mu'awiyata ya bamu labari yace, A'amashu ya bamu labari daga Shaqeeq, daga Ummus-Salamata tace ; Abdurrahman Bn Aufu ya shiga gare ta, yace sai yace;
" Yaa mahaifiyata, ina jin tsoron kada dukiyata ta halakar dani, domin ni nafi kowa dukiya cikin Quraishawa. " Sai tace;
" Yaa dana (my son) ka ciyar , domin na ji Manzon Allah (S.A.W.W) yana cewa;
" LALLE DAGA CIKIN SAHABBAINA AKWAI WANDA BA ZAI QARA GANINA BA BAYAN NA BARSHI ."
Sai na fita, sai na hadu da Umar na ba shi labari, sai yazo ya shiga gareta yace, " INA HADAKI DA ALLAH, INA DAGA CIKINSU ?"
Tace, " A'A, AMMA BA ZAN QARA BAYYANAWA WANI (wannan magana ) BA BAYANKA ."
(MUSNAD AHMAD, CIKIN MUSNADIN MATA).
A wata riwayar kuma yace;
25950- حَدَّثَنَا أَسْوَدُ بْنُ عَامِرٍ ، حَدَّثَنَا شَرِيكٌ ، عَنْ عَاصِمٍ ، عَنْ أَبِي وَائِلٍ ، عَنْ مَسْرُوقٍ ، عَنْ أُمِّ سَلَمَةَ ، قَالَتْ : قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : " مِنْ أَصْحَابِي مَنْ لَا أَرَاهُ وَلَا يَرَانِي بَعْدَ أَنْ أَمُوتَ أَبَدًا " , قَالَ : فَبَلَغَ ذَلِكَ عُمَرَ ، قَالَ : فَأَتَاهَا يَشْتَدُّ ، أَوْ يُسْرِعُ شَكَّ شَاذَانُ ، قَالَ : فَقَالَ لَهَا : أَنْشُدُكِ بِاللَّهِ ، أَنَا مِنْهُمْ ؟ قَالَتْ : لَا ، وَلَنْ أُبَرِّئَ أَحَدًا بَعْدَكَ أَبَدًا
" CIKIN SAHABBAINA AKWAI WANDA BA ZAN GANSHI BA, SHI MA BA ZAI GANNI BA BAYAN NA MUTU HAR ABADAH !"
NAZARI
--------------
Ba a sami wata magana wacce ta qaryata cewa Annabi (S. A. W. W) bai fadi wannan magana ba.
Amma abin nazarin shine, cikin hadisin ba a kawo cewa Annabi (S. A. W. W) ya ambata mata sunayen wadanda ba za su qara ganinsa ba domin bata ambata ba da bakinta.
TAMBAYA
------------------
(1)- Idan kuwa hakane, ya akayi Ummus-Salamata tasan cewa Umar ba ya daga cikin wadanda ba za su qara ganin nasa ba ko da kuwa a ace yana daga cikinsu ba ?
(2)- Menene dalilin da yasa Umar ya zargi kansa har yayi saurin zuwa gare ta don bincike a kansa?
WANNAN DAI TAMBAYA CE DON NEMAN SANI
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
4th October, 2020/ 17th Safar, 1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com